Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa matsalar tsaron da wasu yankunan ƙasar nan ke fama da ita zai zamo tarihi nan bada daɗewa ba.
Buhari ya yi wannan iƙirari ne lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai bayan kammala Sallar Eld-el-Fitr, a Masallacin Barikin Sojoji na Mambilla Barracks da ke Abuja.
Buhari ya isa filin Sallar Idi da misalin ƙarfe 9 na safe, tare da ‘yan rakiya da su ka haɗa da wasu daga cikin iyalan sa, muƙarrabai da hadimai, Ministoci, Shugabannin Hukumomin Sojoji da sauran manyan jami’an gwamnati.
Wannan ne karo na farko da Buhari ya yi Sallar Idi a wajen Fadar Shugaban Ƙasa, tun bayan ɓarkewar cutar Korona a watan Fabrairu, 2020.
Limamin Masallacin Mambilla Barracks, Dehey Shuwa ne ya ja Sallah, inda ya yi wa ƙasa addu’ar samun zaman lafiya.
Liman Shuwa kuma ya yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da yi wa ƙasar nan addu’a.
Da ya ke amsa tambayar manema labarai, Buhari ya ce tabbas batun tsaro a wasu sassan ƙasar na kan hana shi runtsawa da dare.
Sai dai kuma ya ƙara shan alwashin daƙile matsalar tare da kakkaɓe duk wani ɓatagarin da ya kangare ya ke ta’addanci da garkuwa da mutane.
A lokacin watan azumi dai Shugaba Buhari ya riƙa zuwa halartar tafsiri a masallacin cikin Fadar Shugaban Ƙasa.
Da aka tambayi Buhari batun zaɓe mai kusantowa, ya ce zai tabbatar da an yi wa ‘yan Najeriya sahihin zaɓe, karɓaɓɓe ba tare da maguɗi ba.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce Buhari ya riƙa halartar tafsirin domin ƙara samun taƙawar kusantuwa ga Allah (SWT).
Discussion about this post