A halin yanzu dai farashin fetur a ƙasashe da dama na duniya na yin tashin-gwauron-zabon da bai taɓa yi ba. Hakan na faruwa ne saboda rashin samun shi a wadace da ba a yi yanzu a duniya.
Wani sabon rahoto da wani kamfanin binciken ƙwaƙwaf mai suna Zutobi ya fitar ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta 8 a jerin ƙasashen da har yanzu ake sayen litar fetur arha takyaf.
An dai buga wannan bincike a cikin watan Afrilu, inda farashin galan 1 ke daidai da dala 1.82.
Ƙasashen da ke sahun farko a arhar fetur kafin Najeriya sun haɗa da Venezuela, ƙasa mai arzikin fetur da ke Kudancin Amurka a matsayin wadda ta fi arhar fetur.
A Venuzuela dai galan 1 na fetur bai kai Naira 60 ba. Ana sayar da hakan 1 dala 0.11 kacal.
Venezuela ce ta fi kowace ƙasa a duniya yawan ɗanyen mai kwance a ƙasa.
Libya ce ƙasa ta biyu wajen arhar fetur. Libya da Venezuela duk kusan yadda ake shan fetur kaɗan ya ɗara a ce kyauta ake sha.
Daga Libya sai Iran da kuma Syria da Aljeriya da Kuwait, waɗanda dukkan su galan 7 bai wuce Naira 750 ba. Angola da Najeriya duk kusan Naira 1000 ake sayar da galan 1.
Sai dai kuma binciken ya nuna cewa a Hong Kong ake samun gas wanda ya fi na kowace ƙasa tsada a duniya. Daga Hong Kong kuma sai ƙasar da ke take mata baya wajen tsadar gas, ita ce Netherland. Daga nan sai Norwoy
Dala 13.10 ake sayar da lita 1 ta gas a Netherlands.
Daga cikin dalilan da ke haifar da tsadar su ne yawan sanya wa kamfanoni harajin da ake ɗora wa Kamfanoni.
Discussion about this post