Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa cikin duka ƴan takaran da suka fito neman shugabancin Najeriya a APC, ya fi su gogewa.
Osinbajo ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen taro da majalisar sarakunan jihar Bayelsa ranar Alhamis.
” A cikin su duka ƴan takarar shugaban kasa, na fisu gogewa saboda da ni aka yi mulkin kasar nan tun daga 2015 har zuwa yanzu a matsayin mataimakin shugaban kasa.
” Bayan haka ma a wasu lokutta da dama na rike kasar a matsayin shugaban kasa na wucin gadi a lokacin da shugaba Buhari baya nan.
” Wannan su wasu daga cikin dalilan da ya sa na ke ganin waɗannan dama da na samu sun sa na san yadda kasar take da irin abubuwan da za a yi domin a samu nasara da cigaba.
Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ba domin Osinbajo zai fafata ne da gaggan ƴan siyasa waɗanda suma ba kanwan lasa ba. Da yawa daga ciki kinnsu sun rike mukamai a gwamnatance wasun su tun daga jihohin su har zuwa gwamnatin tarayya.
Waɗanda Osinbajo zai fafata da kuwa harda ubangidan sa , Bola Tinubu wanda shine kusan za a ce ke kan gaba wajen waɗanda ake gani za su iya samun tikitin jam’iyyar.
A karshen wannan wata ne za a gudanar da zaɓen fidda gwani kamar yadda hukumar zaɓe ta sanar.
Discussion about this post