Babban darektan sadarwa na cocin Katolika dake Sokoto Christopher Omotosho ya bayyana cewa babu wani mutum mace ko namiji da aka ji wa rauni.
Omotosho ya xe hasalallun matasa sun cinna wa wasu cocina wuta sannan kuma sun babbake wata mota ɗaya da ke ajiye a wata coci.
Cocinan da aka cinna wa wuta kafin jami’an tsaro su iso sun haɗa da Holy Family Catholic Cathedral, sai kuma cibiyar Bakhita Centre, da kuma cocin St. Kevin’s Catholic.
Rabaren Mathew Kukah wanda shine shugaban majami’ar cocin Katolika ya yabawa jami’an tsaro bisa gaggawar kawo dauki da suka yi kafin matasan yi mummunar ta’adi.
Tuni dai gwamnan jihar Aminu Tambuwa ya saka dokar hana walwala a fadin jihar na awa 24.
Marigayi Deborah Samuel ta gamu da ajalinta ne bayan yin kalaman ɓatanci ga Annabin Tsira, SAW.
Bayan saka wannan batanci, sai matasan makarantar Kwalejin Shehu Shagari, suka bita da jifa har ta sheka lahira.