Majalisar Tarayya ta amince tare da aikawa da kwaskwarimar da su ka yi wa Sabuwar Dokar Zaɓe Sashe na 84 (8) na 2022, ta yadda wakilan zaɓen ‘yan takara masu riƙe da muƙaman gwamnati za su samu damar yin zaɓen fidda-gwani, taron gangami da tarukan jam’iyya.
Majalisar Tarayya ta yi wa sabuwar dokar kwaskwarima ce bayan ta yi la’akari da Kudirin da Shugaban Kwamitin Majalisa Abubakar Fulata ya gabatar a ranar Laraba, a Abuja.
Kudirin dai mai suna, “Kudirin Yin Kwaskwarima Ga Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022 Mai Lamba 13”, ya bayar da dama ga wakilan jam’iyya masu riƙe da muƙaman gwamnati su yi zaɓe a lokacin zaɓukan fidda-gwanin ‘yan takarar jam’iyyu.
Idan an tuna, Sabuwar Dokar Zaɓe wadda Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa hannu cikin watan Fabrairu 2022, ta haramta wa masu riƙe da muƙaman gwamnati su yi zaɓen fidda gwani.
Su Wane Ne Masu Riƙe Da Muƙamai?:
Sun haɗa da: Kansilolin mazaɓu da ke ƙananan hukumomi, shugabannin ƙananan hukumomi da mataimakan su, shugabannin jam’iyyu na ƙananan hukumomi 774, ‘yan majalisar dokokin jihohi da ‘yan majalisar tarayya.
Sauran sun haɗa da: Gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugaban ƙasa da mataimakin sa, Shugabannin Majalisar Gudanarwar Jam’iyya, shugabannin jam’iyya na jihohi, na ƙananan hukumomi da sakatarorin su.
Wannan sabuwar doka da aka yi wa kwaskwarima za ta bai wa waɗannan da aka lissafa a sama su yi zaɓen ‘yan takara a zaɓen fidda gwani.
Idan ba a manta ba, Majalisar Dattawa ta amince da wannan kwaskwarima tun a ranar 10 ga Mayu, 2022.
A farkon shekarar nan PREMIUM TIMES Hausa ta riƙa kawo kwatagwangwamar da ta dabaibaye wannan sabuwar doka. Har ta kai an bada wani rahoton da babban lauya Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da yin surunkutumi cikin sha’anin hukuncin kotu.
Babban Lauya mai rajin kare haƙƙi da ‘yancin jama’a Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da damalmala Babbar Kotun Tarayya ta yadda ta bayar da hukunci baddalalle mai cike da tarnaƙi akan matsayar sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.
Falana ya ce Malami ya yi bakam, ya nuna kamar bai ma san akwai wani hukunci ko umarnin kotu wanda na Kotun Tarayya wanda ya haramta masa yin katsalandan a kan dokar. Amma sai ya jajirce cewa shi sai ya yi amfani da umarnin Babbar Kotun Umuahia, wadda ta bayar da umarnin a soke wannan sashen ɗungurugum.
Falana wanda babban lauya ne (SAN), ya fitar da sanarwa inda ya bayar da cikakken bayanin yadda Manyan Kotunan Tarayya guda uku suka bayar da mabanbantan hukunce-hukunce. Daga nan Falana ya ɗora laifin gaba ɗaya a kan Ministan Shari’a Malami.
“Don haka sai Falana ya ce ya kamata Malami ya sani cewa ba fa zai iya yin yadda ya ga dama ba, ta hanyar bin umarnin da ya ga dama, kuma ya bijire wa wadda ya gada dama.
“Sannan kuma babu sauran wata jikara ko tantama, tabbas Ministan Shari’a ya damalmala hukuncin Babbar Kotun Tarayya har ta bayar da baddalallun hukunce-hukunce a kan sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.” Inji Falana.
Discussion about this post