Ƴar takarar shugaban kasa, wato mace ta farko da ta sayi fom ɗin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC Uju Ohanenye ta ce ba za ta bari maza su nuna mata fin karfi ba a wajen gwagwarmayar zama shugaban kasa ba.
Uju ta bayyana cewa da karfinta ta shiga takarar kuma bata tsoron gungun mazajen da zata fafata da su a jam’iyyar.
” Da ƙarfina na fito takara, kada ma wani namiji ya yi min ganin mace ya yi zaton zai iya latsani.
Bayan haka ƴar takarar bayyana wasu hanyoyi da dabaru na cigaba da za ta ɗauka idan ta zama shugaban kasa.
” Kun ga yadda ake ɗebo kamfanonin kasashen waje su zo su rika gina mana hanyoyi, a karkashin mulki na ba za a yi haka. Maimakon haka, katti zan rika sawa na kowacce unguwa su fito su gina hanyoyin su. Idan muka yi haka matasa za su samu aikin yi.
” Zan yi mulki ne a matsayin ƴar Najeriya ba tare da wai na nuna banbancin addini ba, ƙabilanci ko ɓangaranci ba. Kowa zai lashi zuman soyayyata da kuma kishin kasa.
Sai dai kuma a karshe Uju ta ce akwai yiwuwar za ta iya sauka daga takarar idan ta hango wani daga cikin ƴan takaran da yake da kishin kasa da irin akidar ta a siyasance.
Jam’iyyar APC ta saida wa mata da fom din takara akan naira miliyan 50 ne.