Ɗaya daga ƙungiyoyin ƙwadago da ke cikin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago (NLC), wato TUC, ta yi barazanar rankayawa yajin aikin nuna goyon baya ga ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU).
TUC ta ce za ta tafi yajin aikin ne domin tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta cika wa malamai da tsarin ilmin jami’o’i alƙawurran da ta ɗauka, domin a gaggauta buɗe jami’o’i yara su ci gaba da karatu.
Cikin wata sanarwar da su ka fitar wadda kwafen takardar ya faɗo hannun PREMIUM TIMES, TUC ta zargi Gwamnatin Najeriya da laifin yin watsi da ilmin jami’o’i ta bar ɗalibai da ma’aikata cikin halin wahalhalu.
Wannan barazana ta zo kwana kaɗan bayan NLC ita ma ta yi irin wannan barazanar tafiya yajin aikin kwanaki uku, domin nuna goyon baya da ASUU.
A wata sabuwa kuma, Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa (NANS), ta yi alƙawarin hargitsa taron zaɓen fidda-gwani da jam’iyyun siyasa na APC da PDP wanda za a gudanar kwanan nan a Abuja.
A reshen ɗaliban na Kudu maso Gabas kuwa, sun bai wa Gwmnatin Tarayya wa’adin daidaitawa don ɗalibai su yi gaggawar komawa makarantun su.
A sanarwar da TUC ta fitar, wadda Shugaban Ƙungiya Quadri Olaleye, ya yi kira ga gwamnati “ta gaggauta lalubo maganin matsalar da ke tsakanin ta da malaman jami’o’i (ASUU).”
TUC ta zargi Ministan Ilmi Adamu Adamu da Ministan Ƙwadago Chris Ngige da laifin kasa shawo kan matsalar malaman jami’o’i.
A kan haka ne ƙungiyar ta yi kira ga Adamu Adamu da Chris Ngige su yi murabus, domin a naɗa masu kishin ganin ‘yan Najeriya marasa galihun da ba su iya fita waje karatu sun samu na su ilmin nan a cikin gida Najeriya.
TUC ta yi fata-fata da shugabannin siyasa, waɗanda ta ce “sun yi watsi da harkar inganta ilmi, sun makance sun ɗimauce wajen haukan sayen tikitin neman tsayawa takarar shugaban ƙasa har zunzurutun kuɗi naira miliyan 100 kowanen su.”
Farkon makon jiya ne dai ASUU su ka ƙara watanni uku nan gaba su na yajin aiki, tunda a cewar su, Gwamnatin Tarayya ta raina masu hankali.
Discussion about this post