Kungiyar malaman jami’o’in kasarnan sun sanar da cigaba da yajin aiki har na tsawon wasu watanni uku masu zuwa.
Idan ba a manta ba zuwa yanzu ɗalibai sun shafe watanni 3 a gida saboda yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi.
Wannan karin watanni da kungiyar malaman suka yi ya sa dalibai da iyaye a jihar Legas sun fito zanga-zangar kira ga gwamnati da malaman su sasanta ɗalibai su koma makaranta.
Bayan ganawa da ƙungiya malaman ASUU ta yi da mambobinta ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin a jami’ar Abuja, ta yanke shawarar cigaba da yajin aikin na tsawon watanni uku masu zuwa.
Takaddamar da yaki ci yaki cinyewa tsakanin gwamnati da kungiyar malaman ya hada da musamman tsarin yadda za a rika biyan malaman albashi.
Malaman jami’o’in sun turje lallai sai dai gwamnati ta rika biyan su da tsarin UTAS. Ita gwamnati ta kafe cewa lallai sai dai ta rika biyan su ta tsarin biyan albashi na IPPIS.
An naɗa kwamitoci domin a tsara yadda za a shawo kan wannan matsala amma abin har yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba. Daga an fara zama sai kuma abin ya ruguje, ayi barambaram.
A dalilin haka ne ya sa kungiyar malaman suka ce ki dai gwamnati ta amince da zaɓin su ko kuma su cigaba da yajin aiki sai yadda hali ta yi.
Discussion about this post