Yayin da zaɓen fidda-gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa ke ƙara matsowa, jam’iyyar adawa PDP ta yanke shawarar yin watsi da tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya a 2023, inda ta ce ɗan kudu da ɗan Arewa, ɗan gabas ko ɗan yamma duk kowa zai iya fitowa takara.
Babban Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba ne ya bayyana haka, jim kaɗan bayan da Kwamitin Ƙolin PDP ya tashi daga taron Majalisar Zartaswa da suka gudanar a ranar Laraba.
Ya ce an yanke wannan shawarar ce bisa tunanin bin umarni ko yin aiki da shawarar kwamitin tsarin karɓa-karɓa.
“Bayan an yi bayanai masu ƙarfi na tsawon lokaci, NEC na PDP sun amince da shawarar da Kwamitin Karɓa-karɓa na Ƙasa na PDP ya bayar, cewa a bar kowa ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023. Amma idan ta kama, jam’iyya za ta iya sa baki wajen ganin an cimma yarjejeniya tsakanin ‘yan takara, sun fitar da mutum ɗaya a cikin su, ba tare da sun kafsa a tsakanin su, a zaɓen fidda-gwani ba.”
Ya ce an cimma wannan matsaya ce domin shimfiɗa adalci, kuma don a samu isasshen lokacin da ya dace domin kafa tsarin yarjejeniyar karɓa-karɓa a lokaci mafi dacewa, ba tare da tunanin samun cikas ko wata farraƙa ba.”
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP ya ce za a yi gagarimin taron gangamin musamman na zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa a ranakun 28 da 29 Ga watan Mayu a Abuja.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata David Mark ne Shugaban Kwamitin Tsara Gangamin Zaɓen Ɗan Takarar PDP na 2023.
Yayin da Ifeanyi Ugwuanyi ke mataimakin Mark, tsohon Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema ne Sakatare.
Wannan sanarwar yin fatali da tsarin karɓa-karɓa ya zo ne makonni kaɗan Kwamitin Karɓa-karɓa ya miƙa rahoton da ya ƙunshi shawarwarin yin watsi da tsarin karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin Kudu da Arewa.
Idan ba a manta ba, yankin Kudu maso Gabas ya daɗe ya na kartar ƙasa cewa su ya kamata a bai wa mulki a 2023.
Kwamitin karɓa-karɓar PDP dai na mutum 37, a ƙarƙashin shugabancin Gwamna Samuel Ortom ba Jihar Benuwai.
Tuni dai kwamitin tantance ‘yan takarar PDP a ƙarƙashin David Mark ya tantance ‘yan takarar PDP mutum 17, waɗanda su ka sayi fam na neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Discussion about this post