Kotun Koli ta umarci tsohon gwamnan jihar Ribas, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ya bayyana a gaban wata kwamiti wanda gwamnan jihar Nyesome Wike ya kafa domin binciken zargin handame wasu kudade na jihar da suka kai naira biliyan 98.
Tun da farko kotun sauraren kara ta fara yanke hukuncin lallai sai Amaechi ya bayyana a kwamitin da Wike ya kafa da ta bankado harkallar wannan kudade da ake zargin Amaechi da wawushewa amma kuma ya daukaka kara.
A kotun daukaka kara ma Amaechi bai yi nasara ba. Kotun ta yanke lallai sai ya bayyana ya yi bayani akai.
Daga nan sai ya garzaya kotun Koli. A can ma ba ta sake zani ba. Kotun ta yanke hukunci a yau Juma’a cewa lallai dole sai Amaechi ya bayyana a kwanitin nan dai yayi bayani game da zargin da ake tuhumar sa akai.
Zargin handame naira biliyan 98
Ana zargin Amaechi da laifin saida wasu bututun Iskar gas mallakin jihar Ribas ga kamfanin Sahara Energy akan naira biliyan 98 wanda bayanai suka nuna maimakon sune su biya gwamnatin jihar ribas ita gwamnatin Ribas karkashin Amaechi suka suka kamfato wadannan kudade daga asusun jihar suka jibge a asusun su.
A dalilin haka ne ya sa gwamnatin jihar ta kafa kwamiti da zai binciki wannan harkalla.
Rahoton kwamitin bayan bincike ya nuna cewa lallai akwai harkalla da a ka tafka a ciki kuma an samu hannu Amaechi a ciki dumu-dumu a badakalar.
Discussion about this post