A cikin makon jiya ne kotu a Ikeja jihar Legas ta yanke wa faston cocin ‘Anointed Chosen Vessel Ministry’ Michael Oliseh mai shekaru 54 hukuncin daurin rai da rai bayan an kama shi da laifin yi wa wasu tagwaye mata biyu masu shekara 12 fyade.
Alkalin kotun Abiola Soladoye ta ce ta yanke wannan hukunci ne bayyan gamsuwa da ta yi da hujjojin da aka gabatar da suka tabbatar wa kotun cewa Oliseh ya rika lalata da waɗannan ƴan mata.
Abiola ta ce za a rubuta sunan faston a takardan da aka bude domin rubuta sunayen masu aikata ta’asa irin haka na jihar.
Ta kuma yi kira ga iyaye da su daina damka ‘ya’yan su ga mutanen da basu tabbatar da ingancin halayen su ba.
Bayan haka lauyan da ya shigar da karar Olufunke Adegoke ya ce Oliseh ya aikata wannan ta’asa ne tun a watan Nuwanban 2017 a gidansa dake Ago kusa da Okota a garin Legas.
Adegoke ya ce tagwayen sun fara zama da Oliseh bayan mahaifinsu ya kawo su gidan zama saboda za shi jana’izan wani dan uwansa da ya rasu a can ƙauyen su.
“Ashe tun da aka kawo ƴan matan faston ya rika danne su daya baya daya yana lalata da su. Sannan ya gargaɗe su kada su kuskura su sanar wa mahaifin su.
Ya ce asirin fasto ya tonu ne a ranar da wani makwabcinsa ya ga faston yana bin daya daga cikin ƴan matan da gudu sannan yana kokawar ya saɓule mata kamfai.