Tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Basheer Lado, ya ƙaryata surutan da ya ce ana watsawa wai Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarce shi ya janye takarar da zai sake yi a 2023 a ƙarƙashin APC.
Rahoton da Lado ya ƙaryata dai ya ce Ganduje ya umarci tsohon sanatan cewa kada ya nemi takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, kujerar da ya ke a da, amma yanzu Ibrahim Shekarau ne a kai.
Basheer Garba, wanda a siyasar Kano aka fi sani da Basheer Lado, shi ne Sanatan Kano ta Tsakiya tsakanin 2011 zuwa 2015. Amma yanzu tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau ne a kan kujerar.
Cikin wata sanarwa, Lado ya ce abin da kawai ya sani shi ne, ya sanar da ya sanar da Ganduje zai tsaya takara, baya ma ya rigaya ya sayi fam.
Sannan kuma ya ƙara da cewa ya na da duk wata cancantar da ɗan takara zai iya tsayawa zaben sanata kuma ya yi nasara.
Ya ce har gara a ce ya gwagwata a zaɓen fidda-gwani shi da Shekarau, maimakon a ce ya janye wa Shekarau ɗin.
Ya ce a zaɓen 2019 an shawarce shi ya janye wa Shekarau, kuma ya amince ya janye masa. Amma a yanzu da zaɓen 2023 ya zo, ba zai janye masa ba.
“A matsayi na na Musulmi, na rantse da Girman Alƙur’ani Gwamna Ganduje bai umarce ni wai na janye wa Shekarau ba.
“Sannan kuma masu cewa Ganduje ne dama tun da farko ya ce na sayi fam, wannan ma ba gaskiya ba ce.
“Kawai wasu ‘yan jagaliya ne su ka riƙa watsa wannan surutai marasa tushe da makama, don kawai su goga wa ni da Mai Girma Gwamna kashin kaji.” Inji Lado.
“Ni da kai na ne ya yanke wa kai na shawara cewa zan sake yin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, saboda ganin yadda ɗimbin magoya baya na su ka shafe shekaru su na so na sake komawa a Majalisar Dattawa.
“A fili ta ke lokacin da ina Sanata na yi ayyuka 113 a mazaɓa ta, ciki har da Gadar Sama ta Kundila, wadda aka yi a kan naira biliyan 2.5 (Gadar Lado).”
Lado ya ce shi ne salsalar kawo aikin faɗaɗa titin Kano zuwa Katsina, wanda abin haushi inji shi, aikin na tafiyar hawainiya tsawon shekaru bakwai, saboda Lado ɗin ba ya a Majalisar Dattawa.