Fitaccen mai yin sharhi kan siyasa da al’amuran yau da kullum, kuma kwamishina Ilimin jihar Bauchi, Dr Aliyu Tilde ya yi tir da likimon da ƴan siyasan mu suka yi kiwa ya ki cewa komai game da abinda Deborah Samuel ta ce da kuma matsayin su a kai da kisan da aka yi mata
Tilde ya ce babu wani ɗan siyasa da ya fito ya ce komai akai, dukkan su na tsoron kada su samu matsala da mutane saboda siyasa an shiga yanayi na siyasa ne yanzu kowa na neman kuri’an jama’a.
” In ba haka ba ai idan aka duba wannan yarinya Deborah, ba yanzu ta fara haka ba sannan kuma ta tafka ganganci, katoɓara wanda ta yi da gangar ba tare da ta yi nadama ba. Hatta ƴan uwanta dake tare da ita a lokacin da take waɗannan kalamai, sun kwaɓe ta amma ta ki.
” Irin kalaman da ta yi akan Annabi SAW sun kazanta matuka. Babu wanda zai ji abinda ta ce da gadara da yadda ta faɗe su akan fiyayyen hallira SAW sannan kuma a ce an zauna lafiya.
” Kamar yadda ake fitowa ake kushewa da yin tir da kisan da hasalallun matasa suka yi, ya kamata a fito a kuma rika kushe kalaman da ta yi da kuma yin gargaɗi ga sauran matasa da mutane da su rika sara suna dubar bakin garari domin wasu wuraren ba a gitta su ko da wasa ne.
” Ba ga wanda ba musulmi ba, ko musulmi kake ka yi ɓatanci ga Annabi sai ka shiga ruɗanin gaske. Wand su me suka fi yawa cikin wadanda suka rasa rayukansu fiye da waɗanda ba musulmai ba. A Najeriya bai wuce mutum biyu ba irin haka ya afka wa da wannnan sai kuma wanda a tabayi shekaru 30 da suka wuce.
Tilde ya kara da cewa dole fa ƴan siyasa su fito su faɗi gaskiya su daina boye suna rarume rarume.
” Nan ake kashe mutane a kasahen Inyamirai, babu wanda ya fito ya ce komai, sai ma kare na su da suke yi. Menene IPPB ba su yi ba, ga shugaban su Nnamdi Kanu. Shiru kuma ba su dai na ba.
Shugabanni dole su fito su ce ga matsayin su su daina boye wa a bayan fage, sun yi shiru tsit.
Discussion about this post