Mako ɗaya bayan fitaccen lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana ya ce dokar Najeriya ta hana Jonathan sake fitowa takarar shugaban ƙasa, shi kuma fitaccen lauya Mike Ozekhome ya ce dokar Najeriya ta amince Jonathan zai iya fitowa takara a 2023.
Yayin da Falana ya kawo hujja da Sashe na 137 (3) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, shi kuwa Ozekhome ya bijiro da hukuncin da Alƙalan Kotun Daukaka Ƙara su ka bayar cikin 2014, inda bayan sun yanke hukunci, sai Mai Shari’a Abubakar Yahaya ya karanto hukuncin su ka zartas cewa ai shekara ɗaya da Goodluck Jonathan ya ƙarasa bayan rasuwar Umaru ‘Yar’Adua, ba za sa ta cikin wa’adin shekarun da Jonathan zai yi ya na mulki idan aka zaɓe shi ba.
Misali, da Jonathan ya ci zaɓe a 2015, to a ƙa’ida shekaru takwas za a ce ya yi kenan. Amma shekara ɗaya ta 2010 da ya yi, wa’adin ‘Yar’Adua ne ya kammala masa, ba wa’adin shi Jonathan ɗin ba ne.
Haka kuma a wannan jayayyar an baje Sashe na 135 (2) (b) na Kundin Tsarin Mulkin an yi masa wankin babban bargo.
Premium Times ta buga labarin da Falana ya fito ya ce Dokar Najeriya ta haramta wa Jonathan sake zama shugaban ƙasa faufaufau.
Fitaccen lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ba zai yiwu ya sake shugabancin Najeriya ba har abada.
Falana ya ce babu yadda za a yi Jonathan ya ma tsaya takara a zaɓen 2023, ballantana har ya sake zama shugaban ƙasa.
Falana ya ce kundin dokokin Najeriya ya haramta wa tsohon shugaban sake tsayawa takara ballantana kuma a sake rantsar da shi kan mulki.
Lauyan ya yi wannan kakkausan gargaɗin da ƙarin haske ne a ranar Laraba, daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen Jonathan ya gaggauta sauya sheƙa zuwa APC domin a tsayar da shi takara.
Falana ya ce idan Jonathan ya sake fitowa takara, to ai ya karya dokar Najeriya wadda ta ce iyakar zango biyu kaɗai shugaban da aka zaɓa zai yi a dokance.
Jonathan kuwa an rantsar da shi a cikin 2010, inda ya ƙarasa zangon marigayi Umaru ‘Yar’Adua, kuma an rantsar da shi cikin 2011, lokacin da ya lashe zaɓen 2011.
Falana ya ce idan Jonathan ya sake tsayawa takara, to idan ya ci zai kasance shekaru 9 zai yi kenan kan mulki, maimakon adadin shekaru 8 kacal na zango biyu da kundin tsarin mulkin Najeriya ya gindaya.
“Doka ya soke takarar shugaban ƙasa ta 2023 da aka ta raɗe-raɗi kan Jonathan. Domin tunda ya yi shekara ɗaya ta sauran mulkin Yar’Adua, ai kenan zai yi shekaru 9 ka mulki kenan. Wannan kuwa ya saɓa da Sashe na 137 na Kundin Dokokin Najeriya, wanda ya ce shugaban ƙasa zango biyu kaɗai zai yi na tsawon shekaru biyu.”
Falana ya kuma kawo hujja daga Sashe na 137 (3), ya ce Jonathan ba zai iya neman sake neman zama shugaban ƙasa ba har abada.
Falana ya ƙara da cewa duk wani tawili da masu sharhi ko ‘yan siyasa zasu yi, hakan ba zai wanke Jonathan daga haramcin sake tsayawa takara da doka ta yi masa ba.
Kiraye-kiraye Kan Jonathan:
Ko Dai APC Ta Ba Jonathan Tikitin Takara Ko Ta Sha Kunyar Duniya, Ta Faɗi Zaɓe -Ƙungiyar CNPD:
Ƙungiyar Jaddada Zaman Lafiya da Ci Gaban Najeriya (CNPD) ta gargaɗi APC cewa babu tsimi babu wata dabara, kawai idan dai ta na so ta ci zaɓe, to ta bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kawai.
Ƙungiyar ta shawarci APC ta yi amfani da tsohon shugaban ƙasar, wanda ta bayyana cewa shi ne “mafi cancanta” domin mulki ya koma a hannun sa a 2023.
A ranar Litinin ce CNPD ta yi wannan kiran a wurin wani taron manema labarai, a Abuja.
Wannan kiran ya zo ne kwanaki uku bayan da gungun wasu matasa suka iske Jonathan har gida, suka nemi ya fito takara.
Jonathan ya shaida masu cewa har yanzu dai bai yanke shawarar sake tsunduma cikin siyasa har ya nemi takara a ƙarƙashin APC ko wata jam’iyya ba.
Kiraye-kirayen da matasan su ka yi wa Jonathan ba ya da bambanci da na CNPD. Ƙungiyar ta shawarci a matsa wa Jonathan lamba ya amince ya tsaya takarar.
Babban Kodinetan CNPD mai suna Rapheal Okorie ya nuna damuwar sa ganin yadda Jonathan ke jan-ƙafa da ɓata lokacin tsunduma takarar shugabancin ƙasa ɗin.
“CNPD ba za ta sake shantakewa ta miƙe ƙafar ta zauna ba, har sai ta ɗauki matakan ganin ta tababar da ƙudirin ta na ganin Jonathan ya amince ya fito takarar ya tabbata.
An daɗe ana wannan raɗe-radin cewa Jonathan koma takara, kamar yadda Arewa ta tsara, domin ya sake karɓa, ya yi zango ɗaya, sannan mulki ya koma Arewa.
Da yawa na ganin cewa Jonathan zai yi ganganci da da-na-sani. Wasu kuma na ganin cewa idan ya shiga APC ɗin za yi nasara, bisa la’akari da cewa ɗimbin waɗanda Buhari ya bai wa muƙamai ‘yan PDP na lokacin Jonathan, da waɗanda suka canja sheƙa daga PDP zuwa APC suka yi nasara a gwamnoni, Sanatoci da Mambobin Tarayya duk su na nan danƙam cikin APC.
CNPD ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu su karɓi Jonathan hannu bibbiyu, su ba shi takara.