Tsohon ɗan majalisar Tarayya kuma ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna Isah Ashiru ya yi nasara a zaɓen fidda gwamna jihar Kaduna na jam’iyyar PDP.
Ashiru ya doke tsohon gwamna Ramalan Yero, Sani sidi, Haruna Saeed, da Shehu Sani a zaben fidda gwani da aka yi a Kaduna ranar Laraba.
Sakamakon da ka bayyana bayan zaɓen ya nuna kamar haka, Isah Ashiru Kudan ya samu kuri’u 414,
Sani Sidi ya samu kuri’u 260, Mukhtar Ramalan Yero kuri’u 28, Sani Abbas ƙuri’u 15, Haruna Kajuru kuriu 11 sai kuma sanata Shehu Sani da ya samu 2.
Discussion about this post