Chisom Mefor ɗalibar Jami’ar Najeriya ce da ke Nsukka, amma kuma ta na zaune a yankin Abuja. A yanzu haka ta na shekara ta 4 ne a jami’a.
Yarinya ce mai shekaru 22, kuma mai sha’awar rubuce-rubuce da kuma ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha, amma kuma sai ta ƙara faɗaɗa fasahar ta zuwa harkar noma.
Chisom ta ce a yanzu dai karatun ta ya tsaya cak saboda yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ke yi. Amma kuma ta na tsakiyar samun alheri a harkokin noman da ta runguma, tun da ta fahimci yajin aikin ba mai ƙarewa ba ne. Yajin aikin da aka fara tun cikin Fabrairu, har yanzu babu alamomin cimma sasantawa.
Ta ce a harkar noma ne ta fara kaciɓus ɗin gamuwa da alheri a nasibin rayuwa.
“Na fara shiga harkar noma tun lokacin da aka fara zaman kullen korona, a cikin 2020. Na ga a zaune kawai na ke a gida dirshan ba na komai. Daga nan sai na fara kiwon kifi.
“Na fara zuba ƙananan kifaye guda 100 ko ƙasa da haka. Amma akasarin su duk mutuwa su ka yi.
“Abin ya dame ni, har na yi da-na-sani ma kwamfuta laptop na saya da kuɗi na.” Inji ta. Amma sai na daina yin da-na-sani ɗin.
“To cikin watan Disamba, 2021 ne na je wani taro, sai na haɗu da wani mutum wanda manomi ne, kuma ya na fitar da kayan gona ƙasashen waje.
Chisom ta ce a yanzu dai karatun ta ya tsaya cak saboda yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ke yi. Amma kuma ta na tsakiyar samun alheri a harkokin noman da ta runguma, tun da ta fahimci yajin aikin ba mai ƙarewa ba ne. Yajin aikin da aka fara tun cikin Fabrairu, har yanzu babu alamomin cimma sasantawa.
Ta ce a harkar noma ne ta fara kaciɓus ɗin gamuwa da alheri a nasibin rayuwa.
“Na fara shiga harkar noma tun lokacin da aka fara zaman kullen korona, a cikin 2020. Na ga a zaune kawai na ke a gida dirshan ba na komai. Daga nan sai na fara kiwon kifi.
“Na fara zuba ƙananan kifaye guda 100 ko ƙasa da haka. Amma akasarin su duk mutuwa su ka yi.
“Abin ya dame ni, har na yi da-na-sani ma kwamfuta laptop na saya da kuɗi na.” Inji ta. Amma sai na daina yin da-na-sani ɗin.
“To cikin watan Disamba, 2021 ne na je wani taro, sai na haɗu da wani mutum wanda manomi ne, kuma ya na fitar da kayan gona ƙasashen waje.” Cewar ɗaliba Chisom.
“To daga haɗuwa da shi na fara tashi tsaye sosai, har ta kai ina da kaji 96 yanzu haka. Kuma duk sun girma, sun isa sayarwa.”
Chisom ta na kuma kiwon kifi har yanzu. Ta ce kiwon kifi abu ne mai sauƙi, domin a yanzu haka akwai mai kular mata da kandamin da ta gina ta ke kiwon kifin a ciki.
Ta ce iyayen ta ne su ka fara ba ta jarin kiwon kifin da ta fara yi cikin 2020, sai kuma ta haɗa da wasu ‘yan kuɗaɗen ta da ta yi tattali.
“Sai bayan da na yi asarar kifayen a karon farko sannan na ɗauki darasi daga kurakuran da na riƙa yi, waɗanda su ne su ka riƙa haddasa mutuwar kifayen.”
Ta ce a cikin watanni uku ta zuba Naira 600,000, ta yi cinikin 900,000. Kenan ta samu ribar Naira 300,000 kenan.
Sai dai kuma a yanzu ta ce akwai tsada wajen kiwon kaji. Domin abincin kaji da ake sayarwa naira 4,000 cikin 2020, a yanzu cikin 2022 Naira 8,000 ake sayar da shi.
Chisom ta ce har yanzu ba ta kai ga shiga ƙungiyar mata manoma ba tukunna, amma ta na so ta shiga. Kuma ba ta fara samun tallafi ba daga wata ƙungiya ko hukuma ko cibiya.
Discussion about this post