Duk wani ƙoƙarin samun tallafin noma daga gwamnati sai da Rebacca Isaac ta yi domin bunƙasa harkokin noman ta, amma har yau ko ƙwandala ba ta taɓa samu ba.
Matar mai zaune a ƙauyen Peti cikin Ƙaramar Hukumar Kuje da ke yankin Abuja tare da mijin ta da ‘ya’yan su biyu.
Ta ce kayan gonar da ke shukawa ma ramce ta ke karɓowa daga hannun mutane, sai kuma mijin ta da yaran ta biyu masu taya ta aiki.
Duk da Rabecca da ƙawayen ta mata manoma da ke zaune kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja, har yau ba su taɓa samun tallafin noma daga gwamnati ko wata hukuma, cibiya ko bankuna ba.
Matsalar ta farko ita ce suna fama da matsalar rashin samun wasu muhimman bayanan samun tallafi ko lamuni. Wannan kuma ya buɗe ƙofar yadda ake zuwa ana damfarar su, da sunan za a sama masu tallafin noma.
“Wasu mutane sun taɓa zuwa suka damfari kowacen mu naira dubu 10,000, tare da alƙawarin samar masu tallafin noma. Amma shiru ka ke ji.
“Wasu ma an sake zuwa, su ka ɗauki sunayen mu da tantance mu, mu ka ba su kuɗaɗe. Su ma tun da su ka sulale, shiru ka ke ji.”
“Kai har Naira 7000 na biya kuɗi ga masu Shirin FADAMA, amma ban samu komai ba.” Inji ta.
Akwai tanade-tanaden samar da irin waɗannan tallafin noma a yankunan karkara. Amma ƙarancin ilmi da rashin wayewa na janyo masu rashin yin gamo-da-katar na samun alfanun lamunin.
Gwamnati na yin ƙoƙarin ganin mutanen karkara na cin moriyar shirin bunƙasa harkokin noma, ta hanyar aza su bisa turbar yin amfani da bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na zamani.
Wani binciken da EFInA ta yi a cikin 2021 ya nuna cewa kashi 51 cikin 100 ne kaɗai na baligan ‘yan Najeriya ke amfani da bankuna ko cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na zamani irin su POS da bankin intanet, tsarin inshora ko asusun ajiya na fansho.
Hakan ya nuna Najeriya ba ta kai gacin ƙudirin ta na inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta bankuna a 2020 ba kenan. Saboda Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda ya bijiro da tsarin, ya ƙudiri aniyar ganin cewa an samu kashi 70 na masu amfani da tsarin zuwa 2020.
Yayin da mata kashi 45 bisa 100 kaɗai su ka rungumi tsarin, maza kuwa sun kai kashi 56 bisa 100.
Irin waɗannan matsaloli ne su ka sa mata manoma a Peji ƙauyen su Rebacca, ba su samun tallafi daga bankuna ko wasu cibiyoyi, sai dai daga wajen dangin su.
Hakan ita ma wata mai noma mai suna Ihouma Chijioke, wadda ke noman rogo da kiwon kaji, ta shaida wa wakilin mu cewa a wajen mijin ta kaɗai ta ke samun tallafi.
“Da jarin da miji na ya fara ba ni na fara sana’ar noman rogo. Shi kuma kiwon kaji da jarin naira 30,000 na fara. Amma shi jarin noman rogo da naira 10,000 na fara.”
Ita kuma Elizabeth Onyeri da ke zaune a Pegi, ta ce ta taɓa neman lamunin NIRSAL, a ƙarƙashin CBN, amma ba ta samu ba.