Gwamnatin Tarayya ta fara raba wa marasa galihu tallafin naira biliyan 9.24 ga mutane 76,107 a jihar Kebbi a ƙarƙashin Shirin Tura Tallafin Kuɗi ta Asusun Banki (CCT).
Kodinatan Shirin Halima Shehu ta sanar da haka da a lokacin ziyara da ta kai wa gwmanan jihar Atiku Bagudu a Birnin Kebbi.
Halima ta nemi afuwar mutane kan dadewa da aka yi ba a cigaba da biyan kudaden da aka fara raba su tun a watan Satumba kuma a ka dakata a 2019.
“Yanzu tsarin biyan kudaden ya canja inda za a rika biyan marasa galihu kudaden a jihohinsu ne.
“A jihar Kebbi gwamnati za ta biya marasa galihu 76,107 a kananan hukumomi shida da suka hada da Bagudu, Danko, Wasagu, Dandi, Jega da Shanga.
“Marasa galihu za su karbi kudaden tallafi na watanni 26 da ba a biya su ba wanda zai faro daga watan Janairu zuwa Fabrairu 2020.
“A takaice dai gwamnati za ta raba Naira biliyan 9.24 a jihar Kebbi.
Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar babban bankin Najeriya sun tsara Shirin ‘National Social Safety Nets Projects (NASSP)’ domin tallafawa fakirai da talakawan kasar nan ne.
Ta kuma yi kira ga gwamnan da ya tallafa wa shirin domin ganin shirin ya ci gaba a jihar.
Gwamnan wanda mataimakinsa Samaila Yombe-Dabai ya wakilta ya tabbatar cewa gwamnatin jihar Kebbi za ta cigaba da mara wa Shirin baya domin ganin an ci gaba da tallafawa talakawa a jihar.
Discussion about this post