Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta bayyana bankaɗo waɗansu kuɗaɗe har dala miliyan 23.5, waɗanda aka tabbatar makusanta da iyalan tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, marigayi Sani Abacha ne su ka saci kuɗin daga Najeriya su ka ɓoye a Ingila.
An gano kuɗaɗen waɗanda su na daga cikin maƙudan kuɗaɗen Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce an shafe shekaru a cikin 1990s ana jida daga Najeriya ana ɓoyewa ƙasashen waje.
Hukumar Daƙile Laifuka ta Birtaniya ta ce Abacha ne da makusantan sa da iyalan sa su ka riƙa kinshe kuɗaɗen a waje.
Haka dai hukumar ta bayyana a shafin ta na yanar gizo a ranar Alhamis.
Har ila yau NCA ta ce an ƙwato kuɗaɗen ne bayan da Ma’aikatar Shari’ar Amurka wato USDOJ ta bada umarnin a tilasta ƙwace kuɗaɗen, bayan an shafe shekaru kusan bakwai ana karankatakaliyar shari’a.
NCA ta ce a yanzu dai an ƙwace kuɗaɗen kuma an maida su a hannun kulawar Hukumar Harkokin Cikin Gidan Birtaniya, wadda ita kuma tuni ta fara shirye-shiryen damƙa kuɗaɗen a hannun Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Amurka (USDOJ).
Babban Jami’in Kula da Ƙwato Kadarori Billy Beatie ya ce ƙwato dukiyar da manyan ‘yan siyasa da masu mulki ke sayewa babban aiki ne mai muhimmanci kuma babban makamin yaƙi da cin hanci da rashawa.
Discussion about this post