Yayin da aka fara tseren neman hawan kujerar gwamnan Katsina a zaɓen 2023, masu neman tsayawa takarar gwamna da dama sun bayyana domin hawa kujerar da Masari zai sauka a 2023.
Zaratan da su ka fito a ƙarƙashin APC dai duk na hannun daman Gwamna Masari ne, kuma a bisa dukkan alamu, akwai jan aiki a gaban gwamnan dangane da wanda hankalin da zai fi kwanciya ya gaje shi.
Daga cikin waɗanda su ka sayi fam ɗin takara a ƙarƙashin APC jam’iyyar su Masari, akwai mutum biyar na hannun daman gwamnan, cikin har da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa.
Akwai kuma Mataimakin Gwamna Mannir Yakubu, tsohon Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Faruk Joɓe. Sai Shugaban Bankin FMB, Bankin Bada Lamuni na Tarayya, Ahmed Ɗangiwa. Sai kuma Babban Daraktan Hukumar Inganta Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN), Dikko Raɗɗa.
A shekarar 2023 dai Masari zai cika shekaru 73 a duniya. Kuma ya ce daga shekarar ce zai yi zaman sa gida ya huta da kwaramniyar duniya.
“Na je Majalisar Tarayya har Kakakin Majalisa na yi. To me zan koma na yi kuma a Majalisa?
Duk da Masari ba zai tsaya takarar komai a 2023 ba, to amma kuma dole ba zai rasa sa hannu a batun fitar da ɗan takarar da zai so ya gaje shi a zaɓen gwamna a 2023 ba.
A yanzu dai abin da ke damun Masari ba ‘yan takarar PDP ba ne. ‘Yan takarar da su ka bijiro daga APC ne abin damuwar sa.
Har yanzu dai bai fito ya nuna cewa ga wanda ya fi kwanta masa a rai ba.
Wani mai sharhin siyasa a Katsina mai suna Saifullahi Kuraye, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “Masari fa na cikin ƙaƙa-tsara-ƙaƙa. Ba zai so ya yi wasa da wanda zai gaje shi ba. Ba shi ne gwamnan da aka fi yabo ko ya fi kowa a gwamnonin Katsina ba. Kuma ba zai rasa barin baya-da-ƙura ba.”
Ya sha cewa shi babu wanda ya fi kwanta masa a rai a cikin dukkan ‘yan takarar. Tabbas dukkan ‘yan takarar babu wanda bai taimaka wa gwamnan ta wasu hanyoyi daban ba.
Taken Mataimakin Gwamna dai a fastocin kamfen ɗin sa, shi ne “Daga Liman Sai Na’ibi.”
Kafin zaman sa Mataimakin Gwamna, Yakubu ya yi Kwamishinan Gona har tsawon shekara bakwai.
Shi ma Mustapha Inuwa, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Masari a zaɓen 2015, lokacin ya na shugaban APC a Jihar Katsina.
Inuwa shi ne na hannun dama, kuma ya na a gaba-gaban waɗanda duk wata ƙurar da ta taso ta hau jikin rigar gwamna ko a birnin ko a cikin jeji, shi ake tashi ya kakkaɓe ta.
Shi kuwa Joɓe, ana ganin duk wanda ya kasa shawo kan gwamna dangane da wani abu, to Joɓe na zama da gwamnan zai iya shawo kan sa, gamsu da shawarwarin da.
Joɓe na cikin waɗanda ake ganin sun taimaka da kuɗaɗen su a zaɓen 2015 da 2019.
Shi kuwa Raɗɗa sun daɗe da Masari. Shi ne babbar motar jan hankalin matasa da ƙwarewa a kurɗa-kurɗar tuggun siyasar karkasa na Masari tun a 2007.
Raɗɗa ne Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Katsina, kafin Masari ya bayar da sunan sa a naɗa shi Shugaban SMEDAN.