Yayin da guguwar sauyin sheƙa ta murtuke jam’iyyar APC a Kano, har ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje barci mai nauyi, yanzu kuma wasu manya kuma jiga-jigan gwamnati da jam’iyya sun ƙara ficewa daga APC a Kano, su na komawa NNPP, jam’iyyar Kwankwaso.
‘Yan Majalisar Tarayya biyu, Tijjani Joɓe da Badamasi Ayuba, tare da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Ali Makoɗa sun fice daga APC, sun koma NNPP.
Ficewar ta su dai ya tabbatar da cewa manyan ‘yan APC za su tsiyaye daga jam’iyyar su sauya sheƙa, biyo bayan yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsayar da Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna a matsayin ɗan takarar APC, yayin da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, kuma zai yi masa mataimaki a takarar zaɓen 2023.
Sauran waɗanda su ka fice ɗin sun haɗa da Ahmed Muhammadu, Mai Binciken Kuɗi na APC na Jihar Kano; Umar Maitsidau, Shugaban Matasan APC na Kano, kuma tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Makodai da kuma wasu fitattu a siyasar Kano.
Dama kuma tsohon Kakakin Majalisar Kano, wanda a yanzu Ɗan Majalisar Tarayya ne, Alhassan Rurum da Kawu Sumaila da Aminu Garo, duk sun fice daga APC.
Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Ali Makoɗa dama ya aika wa Gwamna takardar ajiye aiki domin ya tsaya takara, amma sai Ganduje ya shawarci shi ya ci gaba da aikin sa, ya ƙi karɓar takardar ajiye aikin da ya aika masa.
Amma a ranar Juma’a ya tabbatar da ajiye aikin sa, kuma ya shaida cewa ya koma NNPP.
Ɗan Majalisar Tarayya Tijjani Joɓe ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya fice daga APC zuwa NNPP, domin ci gaba da samar wa al’ummar Mazaɓar sa ayyukan inganta rayuwa.
Alamomin Watsewar Ɗaurin Tsintsiya A Kano:
A wani labarin alamomin watsewar ɗaurin tsintsiyar APC a Kano, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Mataimakin Kakakin Majalisa ya fice daga APC, ya koma PDP.
Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kano, Zubairu Hamza Masu ya fice daga APC, ya koma PDP.
Ya yi wannan sanarwa ce a ranar Alhamis, inda ya ce ya koma jam’iyyar adawa PDP, a cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban APC na Mazaɓar Masu, cikin Ƙaramar Hukumar Sumaila.
Ya rabbata dalilai na rikice-rikicen da su ka dabaibaye APC da kuma hususan tsagwaron rashin adalcin da ya ce ana shukawa a cikin APC.
Masu ya ce a cikin APC an maida Shiyyar Kano ta Kudu saniyar-ware, ba a bayar da dammamakin da ya kamata a riƙa bai wa yankin kamar yadda dimokraɗiyya ta shimfiɗa.
Daga baya Masu ya shaida wa manema labarai cewa akwai misalin wani rashin adalcin da aka yi wa tsohon Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kawu Sumaila, wanda Masu ya ce shugabanin jam’iyyar APC ne su ka yi masa na Jihar Kano.
“Idan ku ka duba, za ku ga cewa ba a yi wa Kawu Sumaila adalci a zaɓen 2019 ba. Amma mu ka haƙura a lokacin, saboda jam’iyya ta taushi ƙirjin mu.
“To yanzu kuma tuni har mun fara ganin alamomin za a sake maimaita mana rashin adalcin da aka yi mana a 2019. Saboda haka mu ka ga gara tun a yanzu kawai mu yanke matsayar da za mu ɗauka domin gyara wa kan mu rashin adalcin da aka yi mana a baya.” Inji Zubairu Masu.
Idan ba a manta ba, Kawu Sumaila ya tsaya takarar fidda-gwani na ɗan takarar Sanatan Kano ta Kudu a zaɓen 2019. Amma Kabiru Gaya ya kayar da shi, a zaɓen da ɗimbin ‘yan cikin APC da wajen ta su ka yi iƙirarin cewa an zabga wa Sumaila maguɗi. Wasu ma na cewa fashi aka yi masa da rana kata.
Sumaila ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen, amma uwar jam’iyya a Kano ta ba shi haƙuri, ta ce ya karɓi ƙaddara, ta riga fata.
Akwai alamomi masu ƙarfin da ke nuni da cewa Sumaila zai fice daga APC ya koma NNPP, jam’iyyar su Rabi’u Kwankwaso a Kano.
Discussion about this post