Binciken ƙwaƙwaf ya tabbatar wa wakilin mu cewa Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya sayi fam ɗin sake yin takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, daidai lokacin da a gefe ɗaya kuma ya ke neman takarar shugabancin Najeriya duk a cikin PDP.
Yayin da ya bayyana fitowar sa takarar shugaban ƙasa a bayyane, Bala ya sayi fam na sake takarar gwamna a asirce.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai tsaya a sayen fam ɗin sake takarar gwamna kaɗai ba, tuni har ma an tantance shi, an amince ya kafsa da duk wanda ya fito takarar gwamna a zaɓen fidda gwani na PDP.
Bala dai na da ‘yancin sake tsayawa takara domin idan ya yi nasara, zai ƙarasa zangon shekaru huɗu a Bauchi.
Dama dai an raɗe-raɗin cewa Sakataren Gwamnatin Bauchi Ibrahim Kashim ya ajiye aiki ya sayi fam ɗin takarar gwamna ƙarƙashin PDP, bisa yarjejeniyar idan aka kayar da Bala a takarar shugaban ƙasa, sai Kashim ya janye wa Bala ɗin.
Amma kuma majiya ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wannan zancen duk ƙad-da-ƙanzon-kurege ne. Domin Bala dai ya rigaya ya sayi fam na Naira miliyan 50 da kan sa, har ma an tantance shi.
Kada a manta, Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas wanda shi ma ya na cikin sahun masu takarar shugaban ƙasa a PDP, ya ce wasu masu takarar ba da gaske su ke yi ba, domin sun raba ƙafa, sun sayi fam na takarar gwamna ko na sanata
Wannan jarida dama ta buga labarin cewa Bala ya tabbatar zai janye daga takara idan Jonathan ya fito takarar a APC ko PDP, zan janye daga takara.
Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya tabbatar da cewa matsawar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya fito takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin APC ko PDP, to tabbas zai janye saboda shi, domin ba zai iya yin takara da ubangidan sa ba.
Mohammed ya furta haka a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a ranar Lahadi.
Ya ce Jonathan ne ya fito da shi a siyasar Najeriya, don haka ba zai yi masa butulci ba. Ba zai iya haɗa kafaɗa da shi su yi goyayyar takarar neman shugabancin ƙasa ba.