Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa EFCC za ta bincika kuma za ta bi diddagi da zuba ido kan yadda ‘yan takara da jam’iyyu su ka tara kuɗaɗen kamfen da kuma miliyoyin kuɗaɗen da su ka lale su ka sayi fam na takarar zaɓen fidda gwani.
Bawa ne ya yi wannan bayani a lokacin da ake tattaunawa da shi a Gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a, a Abuja.
Ya ce EFCC za ta yi aiki tare da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki a harkokin gudanar da zaɓe, domin EFCC ta bi diddigi dagano yadda ‘yan takara su ka samu kuɗaɗen da su ka sayi fam na takarar zaɓen fidda gwani.
“Idan aka zo batun ganowa ko sa-ido kan kuɗaɗen da jam’iyya ko ‘yan takara, to a nan akwai rawar da INEC za ta taka muhimmiyar rawar haɗa kai da EFCC.”
“Mu abin da ya damu EFCC shi ne gano yadda dan takara ya tara kuɗaɗen sayen fam da kuma yadda ya ke ragabzar kashe kuɗaɗe a lokacin kamfen.
Maƙudan kuɗaɗen sayen fam da APC ta yanka da wanda PDP ta yanka sun yi tsadar da ya harzuƙa tare da fusata ‘yan Najeriya.
Yayin da ake rububin sayen fam ɗin takara APC naira miliyan 100 na takarar shugaban ƙasa, ita kuwa PDP na sayar da na ta kan naira miliyan 40.
Kada A Zaɓi Ɓarayin Gwamnati -Shugaban EFCC:
Bawa ya ce abin da ya fi damun EFCC shi ne ta tabbatar waɗanda su ka wawuri dukiyar gwamnati su ka tara ƙazaman kuɗaɗe ba su karɓi mulkin ƙasar nan ba.
Bawa ya ƙara da cewa babban abin da ke gaban EFCC ta tabbatar cewa waɗanda su ka handama da wawuri kuɗaɗe ta hanyar haramtacciyar hanya ba su tsaya takara ba, ballantana har a zaɓe su ko su kai kan su a kan mulki.
A wani labarin kuma, masu neman tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP da APC sai tururuwa su ke yi, su na sayen fam na naira miliyan 100 na APC da kuma na Naira miliyan 40 na PDP.