Sahihiyar majiya ta tabbatar da cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan zai fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC a cikin wannan makon.
Lamarin yunƙurin fitowar Lawan alama ce ta fitowar wata ‘tauraruwa mai wutsiya’ a cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a APC.
Idan Lawan ya fito takara, zai kasance shi ne ɗan takara na biyu daga Arewa, bayan Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi.
Lawan zai fito ne kafin ranar Juma’a, ranar da jam’iyyar APC za ta rufe sayar da fam ɗin takarar shugaban ƙasa.
Zai ƙalubalanci ‘yan Kudu irin su Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da sauran su da dama.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ce Shugaban APC Abdullahi Adamu ya ce har yanzu APC ba ta tsayar da matsaya takamaimai ba kan karɓa-karɓa, wanda tuni ake gani cewa a tsarin, ɗan kudu ne zai yi wa APC takarar shugaban ƙasa.
Majiya ta shaida wa wannan jarida cewa Sanata Lawan ya shafe watanni ya na tunani, nazari da tuntuɓa domin yiwuwar tsayawar sa takarar shugaban ƙasa. Kuma ya na samu daga mutane masu yawa, waɗanda ke matsa masa lambar fitowa takara.
Sanata Lawan dai tun cikin 1999 ya ke a majalisa, har yau.
Kafin ya zama sanata, ya yi Mamba na Majalisar Tarayya tsawon shekaru 8, daga nan kuma tun 2007 ya ke Sanata har yau.
An zaɓe shi Shugaban Majalisar Dattawa cikin 2015.