Yayin da ranakun zaɓen-fidda-gwanin jam’iyyun siyasa don fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa ke ƙaratowa, tabbas wasu ‘yan takarar za su janye ne a cikin wannan makon, ganin yadda gaba-ɗayan karafkiya da cukumurɗar siyasar ta koma a cikin gida.
A ƙarshen makon nan ne APC da PDP za su yi zaɓen su na fidda-gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa a Abuja.
PDP na da ‘yan takara 15, ita kuwa APC na da 25.
Da alamu a PDP ɓangaren kudancin ƙasar nan, sun ɗauki matsaya ɗaya, tun bayan da jam’iyyar ta ce kowa ma ya fito ko daga wane yanki ya ke, babu maganar tsarin karɓa-karɓa.
A APC kuwa mutum 28 ya sayi fam na takarar Shugaban Ƙasa. Amma mutum uku ba su maida fam ɗin ba, wanda aka riƙa sayarwa Naira miliyan 100.
Minista Chris Ngige, Gwamnan CBN Godwin Emefiele da Minista Timipre Sylva duk ba su mayar da fam ɗin da aka ce an saya a madadin su ba.
Sai dai kuma akwai ɗaure kai a jawabin. Saboda Shugaban Bankin Bunƙasa Afrika Akinwunmi Adesina bai je ya ɗauki fam ɗin sa ba. Shi kuma tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan bai tantance barcin makaho ba har yanzu.
Idan Akinwunmi ya nesanta kan sa, Jonathan ma ya noƙe, kenan saura ‘yan takara 23 a APC.
Sai dai kuma bisa dukkan alamu, akwai yiwuwar ‘yan takara da dama za su janye su bar wa wasu, domin har sun fara ƙulla ƙawancen yin hakan.
Batun Cimma Daidaiton Tsayar Da Ɗan Takara Ɗaya Kudu Maso Yamma:
Yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ke magana da wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa a Osogbo, babban birnin Jihar Osun, ya ce nan ba da daɗewa ba yankin Kudu-maso-yamma zai fitar da ɗan takara ɗaya, ta hanyar cimma matsaya ko yarjejeniya.
Daga yankin dai akwai Osinbajo, Bola Tinubu, Kayode Fayemi, Ibekunle Amosun, Dimeji Bankole da Tunde Bakare duk daga APC.
Dama kuma tun a farkon Mayu ne sun yi irin wannan taron a yankin.
A PDP kuwa, ‘yan takara daga Kudu maso Gabas sun yi taron ƙoƙarin cimma yarjejeniya, yayin da Arewa ƙoƙarin hakan ya gamu da cikas, lokacin da wata ƙungiyar dattawa ta ce ta tsayar da Bukola Saraki shi da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi.
Atiku Zai Sake Jaraba Sa’a Shi Da Peter Obi?:
A wannan makon kuwa lamarin zai sauya baki ɗaya. Saboda ana raɗe-raɗin cewa Atiku zai sake ɗaukar Peter Obi ya yi takarar Mataimakin shugaban ƙasa ga Atikun, kamar dai yadda su ka yi a 2019.
Sai dai kuma wata majiya na cewa Atiku na ganawa da gwamnonin PDP, waɗanda idan har Atikun ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, to ya ɗauki mataimaki daga cikin gwamnonin.
Yunƙurin ‘Yan Takarar Ƙananan Jam’iyyu:
Mutum bakwai ya sayi fam na jam’iyyar ADC kan kuɗi Naira miliyan 25. Daga cikin su akwai Kingsley Moghalu, toshon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin CBN, wanda ko a zaɓen 2019 sai da ya yi takara a ƙarƙashin YPP.
Fafarniya Da Nacin Da Sanata Ahmad Lawan Ke Yi Kafin Zaɓen Fidda-gwani:
Sanata Ahmad Lawan ne na ƙarshen fitowa takara da sayen fam a APC. Da ya ke jawabi a Daura, Lawan ya ce turo shi aka yi domin ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Ya ce abokai da abokan arziki ne su ka matsa masa lambar fitowa takara.
A hakan kuma ya ce tabbas ya cancanci fitowa, kuma ya na da laƙanin iya yi wa Najeriya kyakkyawan riƙon shugabanci.
Yaƙin Neman Zaɓe Sai Mai Jirgin Rangadin Ƙasa:
Idan ɗan takarar shugaban ƙasa ba shi da jirgin kan sa, wanda zai riƙa zirga-zirgar ziyarar jihohi ya na sagarabtun nan haɗin kan masu zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa, to kuwa tilas sai ya tanaji jirgin da zai ɗauka shata.
Saboda kusan dukkan manyan ‘yan takarar sun ƙaurace wa zirga-zirga kan titunan ƙasar nan, bisa alama saboda matsalar tsaro.
Wani rahoto ya nuna yadda wasu gwamnoni 9 su ka kashe maƙudan miliyoyin kuɗaɗe domin gararambar neman kujerar shugaban ƙasa, tun ma kafin zaɓen fidda-gwani.
Gwamnonin da ke takara a ƙarƙashin APC da PDP sun haɗa da Nyesom Wike na Ribas, Kayode Fayemi na Ekiti, Aminu Tambuwal na Sokoto, Bala Mohammed na Bauchi, Emmanual Udom na Akwa Ibom, Ben Ayade na Cross River, Dave Umahi na Ebonyi, Mohammed Badaru na Jigawa da Yahaya Bello na Kogi.
‘Ga Gani, Ka Gani Ƙwalelen Ka’: Yadda Gwamnoni Ke Wa ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa Ƙwalelen ‘Daligets’:
A makon jiya Jihar Kaduna ta ce masu zaɓen ‘yan takarar jihar su na goyon bayan Bola Tinubu.
Amma kuma kwana biyu sai Gwamna El-Rufai ya ce su jihar Kaduna za su zaɓi Rotimi Amaechi ne.
Tsakanin Amaechi Da Tinubu: Wa Wakilan Jigawa Za Su Zaɓa?
Yadda Tinubu Ya Taimake Ni Na Zama Gwamnan Jigawa -Badaru:
Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa ya yi bitar tunin yadda tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya taimaka aka kafa jam’iyyar APC, wadda albarkacin ta ne shi Badaru ya zama gwamna a Jigawa cikin 2015.
Da ya ke jawabi a gaban wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na jihar Jigawa a ranar Juma’a a gaban Tinubu, Badaru ya ce da taimakon da Tinubu ya yi wa jam’iyyar ne ta kai shi ga samun nasara a Jihar Jigawa, cikin 2015.
“Mun nemi jam’iyyar da za mu shiga takarar gwamna cikin 2011. Asiwaju Bola Tinubu ya samar min jam’iyya. Na shiga zaɓe, na zo na biyu.”
Badaru ya ce duk da ya haɗu da ƙalubale a 2011, amma dai goyon bayan da ya samu a lokacin ne ya ƙara masa ƙaimin samun nasara a zaɓen 2015.
Badaru ya ce ya na cikin mutane ƙalilan waɗanda za su iya shiga har cikin ɗakin kwanan Tinubu, su tashe shi daga barci.
Ya ce akwai alaƙa mai ƙarfi da shaƙuwa ta ƙut-da-ƙut a tsakanin sa da Tinubu.
Ya ce su a Jigawa ‘yan ga-ni-kashe-nin Shugaba Buhari ne. Kuma za su iya yin duk abin da Buhari ya ce su yi. “Amma fa in dai son Buhari ne a ƙasar nan, to ba wanda ya kai Tinubu son Buhari.”
Ya ce duk wasu surutai da ake yi kan titi, na shirme ne, domin babu wanda ya san iyakar alaƙar da ke tsakanin Buhari da TInubu.
Jawabin Tinubu A Jigawa: Zan Kayar Da Badarun Ku A Wurin Zaɓen Fidda Gwani, Ku Zaɓe Ni Kawai:
Da ya ke jawabi, Tinubu ya ce duk da ya san Badaru ya fito takara, to zai kayar da shi a zaɓen fidda gwani. Don haka su zaɓe shi kawai.
Wannan furuci na sa ya birge ɗimbin jama’ar da ke wurin ana ta kuwwa da tafi. Wasu na “Sai Asiwajun Legas”. Sai Jagaban Bargu.”
“Gwamna Badaru ɗan uwa na ne. Tare mu ka fara ACN. Hakan ba ya na nufin ba za mu iya yin takara ba. Ni da shi kamar tagwayen da aka haifa manne da juna ne. Ba mai iya raba mu sai ƙwararren likita.”
Kalaman Badaru Kan Tinubu Sun Yi Karo Da Furucin Sa Kan Amaechi:
2023: Ba Zan Iya Takara Da Amaechi Ba, Saboda Ni Da Shi ‘Uban Mu’ Ɗaya -Gwamna Badaru:
Gwamna Muhammad Badaru na Jigawa ya bayyana cewa ba zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa shi da Rotimi Amaechi a ƙarƙashin APC ba.
Da ya ke jawabi gaban wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa a Dutse, a gaban Amaechi, Badaru ya ce a shirye ya ke ya janye wa Ministan Sufurin Najeriya takara, shi Badaru ɗin ya haƙura.
“Wasun ku na san sun fara tunanin cewa Badaru ma ɗan takarar shugaban ƙasa ne. To amma ina tabbatar maku cewa ba za a yi takara tsakani na da Amaechi ba, saboda ni da shi uban mu ɗaya (Shugaba Muhammadu Buhari). Kuma duk mu na girmama uban na mu. Na tabbata kuma za mu tafi ne a kan turba da alƙibla ɗaya.
“Ni da shi duk yaran Shugaba Muhammadu Buhari ne, kuma ya na son mu ƙwarai da gaske. Don haka duk abin da za mu yi, sai da neman tubarrakin sa.
“Don haka ku wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na APC na Jigawa, idan ku ka tuna da ni, to kuma ku tuna da Amaechi, saboda ni da shi duk ‘ya’yan Buhari ne.
“Saboda haka a ranar zaɓen fidda-gwani, ko dai na fito takara, ko kuma shi ya fito. Amma dai tabbas ba zan iya yin takara da shi ba, gara na janye masa.”
Tun da farko tsohon Minista Amaechi ya roƙi wakilan zaɓen ‘yan takarar APC na Jigawa su zaɓe shi, saboda ya cancanta. Ya ce ya fi sauran ‘yan takara sanin Najeriya.
Ya ce idan za a kalle shi, to a dube shi da abin da ya yi a baya, ba abin da ake yaɗawa a matsayin ji-ta-ji-ta a kan sa ba.