Jihar Kaduna ta kasance wadda ke ci gaba da kasancewa wata hedikwatar dambsrwar siyasar Arewa. Hakan kuwa na da nasaba da kasancewar Kaduna tsohuwar Hedikwatar Arewa, kafin a daddatsa shiyyoyin Najeriya zuwa jihohi daban-daban.
Jihar ta kasance a rabe, cike da bambanci na ƙabila da addini. An yi gwamnoni 20 a Kaduna, waɗanda 9 a cikin su na farar hula ne, sauran kuma sojoji ne.
A baya Kaduna ta kasance idan gwamnan farar hula Musulmi ne, to mataimakin sa zai kasance Kirista ne.
Amma a 2019 Gwamna El-Rufai ya karya wannan daɗaɗɗiyar al’ada, inda ya ɗauki Musulma Hadiza Balarabe ta zama mataimakiyar Gwamna.
APC a Kaduna ba ta da manyan rigingimu wajen fidda ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023. Dalili kuwa shi ne yawancin waɗanda ba su shan inuwa ɗaya da Gwamna El-Rufai duk sun fice daga jam’iyyar.
Alamomi sun nuna cewa ba wani zaɓen ‘yan takara mai tsauri za a yi wajen fidda gwanin takarar zaɓen ɗan takarar gwamna ba. Kawai dai wani taro ne na jaddada goyon baya ga Sanata Uba Sani, wanda shi Gwamna El-Rufai ke so ya gaje shi.
Uba Sani kafin zaman sa Sanata, shi ne Mashawarcin Gwamna a Fannin Siyasa daga 2015 zuwa 2019.
A ranar 22 Ga Maris Sani ya ƙaddamar da takarar sa a Sakatariyar APC ta Kaduna, inda ya ce zai ci gaba da irin ayyukan da El-Rufai zai tafi ya bari.
Mohammed Dattijo, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kaduna ya fito takarar gwamna shi ma, amma aka ce ya haƙura ya bar wa Uba Sani.
Ja-in-jar Takarar Gwamna Da Sani Sha’aban, Surikin Buhari:
Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Sani Sha’aban, wanda ɗan sa Turad ke auren Hanan Muhammadu Buhari, autar Buhari kuma autar A’isha Buhari, ya yi ƙemadagas ya ce ba zai janye wa Uba Sani ba.
Sha’aban bai ji daɗin yadda El-Rufai ya nuna Uba Sani ya ce a bar masa takara ba.
“Ni ba zan shiga ruguguwar naɗa wani halifan gwamna ba. ‘Ya’ya na da kan su su ka sai min fam na takarar gwamnan Kaduna a ƙarƙashin APC, na naira mijiyan 50. Saboda haka wannan ba abin wasa ba ne. Da na janye har gara a fito a kafsa zaɓen fidda gwani kawai, shi ne magana.” Inji Sha’aban.
Sha’aban na tunanin samun goyon baya daga manyan ‘yan siyasar da ke kusa da surikin sa Shugaba Buhari.
Majiya ta ce Sha’aban zai samu goyon baya sosai daga fadar shugaban ƙasa.
Amma dai a yanzu alamomi na nuni da cewa Uba Sani ne ke da tasiri a zaɓen fidda gwani.
Sai sai kuma Uba Sani zai ci karo da matsaloli biyu. Magoya bayan Sani Sha’aban ka iya yi masa fancale su zaɓi Isa Ashiru na PDP a zaɓen gwamna.
Shi ma Isa Ashiru zai yi bakin ƙoƙarin ganin ya yi nasara, musamman tunda ya daɗe ya na maitar ganin ya zama gwamnan jihar Kaduna.
A ɓangaren PDP, Isa Ashiru Kudan ya yi nasarar zama ɗan takarar gwamnan Kaduna, bayan ya kayar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero da wasu.
Shehu Sani wanda ya ƙi bai wa wakilan zaɓen ‘yan takara ko sisi, ƙuri’ar mutum biyu kaɗai ya samu.
Datti Ahmed Shugaban Jami’ar Baze University ta Abuja, tuni ya janye takarar, ya ce rashin mutuncin da ake yi wajen sayen wakilan zaɓen ‘yan takara ya kashe duk wata darajar dimokraɗiyya.
Discussion about this post