Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar matakan hana aukuwar fashewar abubuwa da kuma rugujewar gine-gine a ƙasar nan.
Ta yi kiran ne sakamakon fashewar silindar iskar gas da ta faru a unguwar Sabon Garin Kano har ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Hukumar Gudanar da Aikin Agajin Gaggawa (NEMA), wadda ke ƙarƙashin ma’aikatar ta Sadiya, ta bayyana tun da farko cewa wani gini ya ruguje a sanadiyyar fashewar gas ɗin, kuma an tsamo gawarwakin mutum tara daga cikin bulullukan rusasshen ginin wanda ke daura da inda gas ɗin ya fashe.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa ministar kan aikin jarida ta bayar, wato Nneka Ikem Anibeze, an ruwaito Hajiya Sadiya ta na bayyana alhini kan faruwar lamarin, yayin da kuma ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gwamnatin Jihar Kano.
Ministar ta bayyana al’amarin da cewa wani abu ne mai ƙona rai kuma ibtila’i ne, har ta ƙara da cewa: “Wannan abin baƙin ciki ne. Iskar gas ta fashe, gini ya ruguje, kuma mutane da dama da abin ya ritsa da su sun rasu, sannan ana faman ceto wasu daga cikin bululluka da rodin ginin… wannan babban abin baƙin ciki ne.
“Ina jajanta wa iyalan waɗanda su ka rasu da kuma gwamnatin Jihar Kano.
“Yawaitar aukuwar fashewar abubuwa a ƙasar nan a cikin ‘yan kwanakin nan ta na da ban-tsoro, kuma mu na kira ga hukumomin da su ka kamata da su yi wani abu da sauri don hana ci gaba da aukuwar fashe-fashe da rugujewar gini a ƙasar nan.”
Darakta-Janar na NEMA, Alhaji Mustapha Habib Ahmed, ya tura motocin haƙar ƙasa kuma ya riƙa bada umarni wajen aikin ceton rai a wajen da abin ya faru tare da haɗin gwiwar hukumar agajin gaggawa ta jihar, wato SEMA, da ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya, da hukumar ‘yan sanda, da hukumar tsaron lafiyar ƙasa (Civil Defence) da sauran masu kai agaji don tabbatar da an ceto mutanen da ginin ya zube a kan su tare da kai su asibiti don a yi masu magani.
Bayan fashewar gas ɗin dai, an riƙa yaɗa ji-ta-ji-ta a soshiyal midiya cewa wai bam ne ya tashi, har sai da hukumar ‘yan sanda ta ƙaryata labarin.
Kwamishinan ‘Yanda na Jihar Kano, Alhaji Sama’ila Dikko, ya fito ya ce, “Ba bam ba ne ya tashi, silindar gas ce ta fashe. Mun san hakan saboda wani mutum wanda ya na cikin waɗanda abin ya fara ritsawa da su wani mai walda ne a wannan yankin.
“Mutum huɗu sun rasa ran su, waɗanda sun haɗa da maza biyu da mace ɗaya, amma ba mu sami ɗalibi wanda fashewar ta ritsa da shi ba.”
Discussion about this post