‘Yan ta’addar da su ka kai wa jirgin ƙasa hari tsakanin Abuja zuwa Kaduna, sun sako ɗaya matar mai ciki da su ka yi garkuwa da ita, bisa dalilai na tausaya mata.
An ruwaito cewa an sako matar ce wadda ba a bayyana sunan ta ba, saboda laulayin cikin da ke damun ta, su ka tausaya mata.
Maharan sun kama su a ranar 28 Ga Maris, bayan sun kashe mutum 9 a cikin jirgin, kuma su ka yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da mata biyu masu tsohon ciki. An kama su tsakanin Rijana da Katemari, wajen ƙarfe 8 na dare bayan an ji wa da dama raunuka.
Bayan kwanaki me a cikin azumi su ka saki Shugaban Bankin Manoma na Ƙasa, Alwan Hassan, bayan an biya maƙudan kuɗaɗen fansa.
Cikin wani bidiyon minti biyu, an nuno mai cikin ta na magana cewa ‘yan ta’addar sun mutunta su kuma sun riƙe su da daraja.
Ta ce sun riƙa ciyar da su da kuma kula da magunguna sosai.
Ta kuma tabbatar da cewa an bari sun yi azumi, kuma wanda duk ba shi da lafiya, ana kula da magungunan sa sosai.
Mai cikin ta kuma tabbatar cewa haƙiƙa ɗaya mai cikin ta haihu a sansanin ‘yan ta’adda ɗin.
“Ina kira ga Gwamnati ta duba halin da sauran waɗanda ake tsare da su ɗin ke ciki a daji, ta saurari ƙorafin da ‘yan ta’addar ke yi.”
Duk da dai ‘yan ta’addar ba su bayyana buƙatar da su ke so a biya masu ba, masu nazari ciki har da wani malamin tarihi a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto, mai suna Murtala Ahmed-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kaduna sun san dukkan buƙatun da maharan ke neman a biya masu.
Ya ce bincike ya tabbatar cewa su Dogo Giɗe da Ali Kawajo ne su ka shirya kai wa jirgin hari da kuma yin garkuwa da fasinjojin.
Ya ce Gungun su Giɗe da Kawajo na da alaƙar ƙut da ƙut da Ansaru da kuma Boko Haram.
“Dogo Giɗe ya daɗe idan ya kama mutanen a ke da kusanci da gwamnati ko dangin jami’an gwamnati, ya kan nemi a biya masa wata buƙatar daban, ba ta kuɗi ba.
Akwai kwamandojin sa da jami’an tsaro su ka kama kuma yake so a sake su. Ko lokacin da ya yi garkuwa da ɗaliban kwalejin Yauri, ba kuɗi ya nema ba, amma nema ya yi a sako masa yaran sa da aka kama, shi kuma zai saki ɗaliban.” Haka Murtala ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Yadda Ɗaya Mai Cikin Da Aka Yi Garkuwa Da Ita Ta Haihu A Sansanin ‘Yan Ta’adda:
A ƙarshen watan Afrilu ne rahotanni su ka tabbatar cewa ɗaya daga cikin matan da ke hannun masu garkuwa da fasinjojin da aka kama a harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, ta haifi jinjira a sansanin ‘yan ta’adda.
An dai yi garkuwa da su tun a ranar 28 Ga Maris, 2022, bayan an buɗe wa jirgin ƙasan wuta, ya tsaya.
Sun shafe wata ɗaya cur a hannun masu garkuwa da su, duk kuwa da kiraye-kirayen da jama’a ke yi cewa gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin ceto su.
Kwanan bayan ‘yan ta’addar sun saki bidiyo biyu, inda su ka nuno waɗanda ke tsare a hannun su, har su na jawabin a gaggauta ceto su ta hanyar sasantawa da waɗanda ke tsare da su.
Bidiyon ya ɗan kwantar da hanulan iyalan waɗanda ke tsare, inda su ka samu tabbacin ba a kashe waɗanda aka tsare ɗin ba.
To amma kuma murna ta koma ciki, ganin yadda ‘yan ta’addar su ka gindiya wa gwamnatin tarayya tsauraran sharuɗɗan da sai an cika masu sannan za su sake su.
Duk da dai ba a fito an ce ga sharuɗɗan ba, amma rahotanni sun nuna cewa su na so ne a saki wasu gaggan ‘yan ta’adda ne su 16 da ke tsare.
Makonni biyu da su ka gabata, Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin ganin ta ceto waɗanda ke tsare ɗin. Sai dai kuma har yau shiru ka ke ji, domin ga shi har mai tsohon ciki daga cikin waɗanda ke tsare ɗin ta haihu a hannun su.
Rahotanni sun tabbatar da haihuwar mai tsohon cikin, wadda ɗaya ce daga cikin mata biyu masu cikin da ke hannun ‘yan ta’addar.
Majiya ta ce ‘yan ta’addar sun kai wa matar likitoci da nas-nas da kayan da mai haihuwa ke buƙata a cikin daji, domin tabbatar da cewa ta haihu lafiya.
Tun cikin makon jiya ta haihu, aka sai a ranar Laraba dangin ta suka samu labari, yayin da ‘yan ta’addar su ka aika masu da sanarwar haihuwar ta.
Dangin matar sun ce an kai mata likitoci da nas-nas da kayan agajin mai haihuwa, inda ta haihu a bisa kulawar likitoci.
Sun ce ‘yan ta’addar na neman a sako wasu kwamandojin su kafin su saki wadanda ke a hannun su.
“A cikin makon nan suka sanar da mu haihuwar ta. Amma ba a ce mana mace ta haifa ko namiji ba.” Haka majiya daga cikin dangin ta ta tabbatar.
Mu Na Ƙoƙarin Ceto Matafiyan Jirgin Ƙasa Da Ke Hannun ‘Yan Ta’adda -Gwamnatin Tarayya:
Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed ya ce ba za mu shaida wa ‘yan jarida ƙoƙarin da gwamnati ke yi don ceto waɗanda aka kama ba.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta na yin dukkan ƙoƙarin da ya dace wajen ganin ta ceto dandazon fasinjojin jiragen da aka yi garkuwa da su a dajin Kaduna, ciki watan Maris.
Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana wa manema labarai haka a Faɗar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, a ranar Laraba.
Mohammed ya ce duk da dai ba zai bayyana wa ‘yan jarida takamaiman irin ƙoƙarin da ake yi ba, “amma dai ina tabbatar ma ku da cewa a yanzu ɗin nan da mu ke magana, ɓangaren gwamnati daban-daban na can na yin ƙoƙarin ganin an ceto mutanen da ran su da lafiyar su.”
Minista Lai Mohammed ya ƙara da cewa “abin da gwamnatin tarayya ke yi ba abu ba ne da za a fito a wurin taron manema labarai ana yayata shi ba.
Ya ce musamman saboda akwai butun rayuwar waɗanda ake tsare da su, kada lamarin ya dagule masu.
“Amma dai ɓangarorin jami’a tsaro da dama na aiki ba dare, ba rana domin bin-diddigin yadda harin da garkuwar su ka faru domin lalubo yadda za a ceto su da ran su da lafiyar su.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka kai wa jirgin hari a ranar 28 Ga Maris, bayan jirgin ya bar Abuja, kan hanyar sa ta zuwa Kaduna, tsakanin Katari.
Aƙalla mutum 8 aka bada rahoton mutuwar su.