Wata kotun Tsibirin Jersey ta tabbatar da cewa ta ƙwato fam miliyan 1.9 daga hannun wani tsohon Janar na Sojojin Najeriya, Jeremiah Useni, waɗanda ya ɓoye a ƙasar.
Kotun ta yi wannan sanarwar a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Bailwick Express ta Tsibirin ta ruwaito.
Kotun Royal Court ta ƙwace kuɗaɗen ne daga asusu huɗu waɗanda ke Standard Chartered Bank, da aka ajiye su tsawon shekaru fiye da 15, wato tun daga cikin 1986 lokacin da Jeremiah Useni ya buɗe asusun da sunan “Tim Shani”.
Tuni dai aka gano cewa Tim Shani sunan bogi ne, wanda tsohon Ministan Abuja na lokacin mulkin marigayi Sani Abacha ya ke amfani da shi, ya na kimshe kuɗaɗen sata.
Useni mai shekaru 79, ya kasance Janar mafi kusanci da marigayi Sani Abacha, kuma ya yi Ministan FCT Abuja a lokacin.
Tsakanin 2015 zuwa 2019 kuma ya yi Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.
Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro ya binciki Jeremiah Useni, kuma ya same shi da laifin satar kuɗaɗe.
Rahoton wanda yanzu haka ya na hannun PREMIUM TIMES, ya samu Useni da laifin mallakar maka-makan rukunin gidaje, gidan mai manyan kadarorin da ba a faɗi iyakar su ba.
An dai tabbatar da cewa, “ya tara wannan dukiya da kuɗaɗen sata ne.”
An samu Tim Tali Hotels, Tali Farms a Gwagwalada da sauran. Kuma sunayen kadarorin sun yi daidai da sunan da ya raɗa wa kamfanin sa da ke Tsibirin Jersey.
Cikin 2001 Standard Chartered Bank na Jersey ya rubuto wa Useni wasiƙa da sunan sa na bogi, wato Tim Shani.
A cikin wasiƙar sun nemi ya aika masu da hotunan sa. Useni bai maida masu amsa ba har sai bayan watanni shida, Jeremiah Useni ya maida masu amsa, kuma ya ci gaba da kiran kan sa “Shani”.
A cikin amsar da ya bayar, Useni ya nemi bankin ya maida masa kuɗaɗen cikin asusun wani banki a Najeriya. Amma Standard Chartered Bank ya ƙi yarda.
Wannan roƙo da Useni ya yi ne ya sa a cikin 2003 jami’an tsaro su ka yi zargin kuɗin na sata ne, sai aka kulle asusun, aka ƙwace kuɗaɗen.
Bayan lauyan Jeremiah Useni ya shafe shekaru huɗu ya na kiciniyar a sakar masa kuɗaɗen, amma Gwamnatin Tsibirin Jersey ta ƙi, a ƙarshe dai cikin 2007 sai Useni ya fito ya bayyana gaskiya cewa shi ne Tim Shani ba wani ba.
Daga nan kuma aka nemi ya bayar da cikakken bayanin irin sana’a da kuɗaɗen da ya ke samu a shekarun 1980 zuwa cikin shekarun 1990, har ya ajiye waɗancan kuɗaɗen.
Lauyoyin Jersey sun haƙƙaƙe Jeremiah Useni ya ɓoye sunan sa ne saboda kuɗaɗen na sata ne. Daga nan aka maida kuɗaɗen cikin Asusun Tara Kuɗaɗen Da Aka Ƙwato Daga Manyan Ɓarayi na Tsibirin Jersey.
Lauyan Useni ya yi ƙoƙarin shaida wa kotu cewa Useni ya samu kuɗaɗen ne ta hanyar alheri da kyauttttukan da abokai da abokan arziki su ka riƙa yi masa a baya. Amma kotun ba ta gamsu ba.
Bayan kotu ta ƙwace kuɗaɗen, ba ta bayar da umarnin a maida kuɗin ga gwamnatin Najeriya ba.
PREMIUM TIMES ta kira wayar Jeremiah Useni, kuma ta tura masa saƙon tes, amma har zuwa ranar Juma’a bai amsa ba.
Discussion about this post