Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefile ya bayyana cewa duk masu yin cecekuce kan cigaba da zamansa gwamnan babban bankin Najeriya, sun bi a hankali fa kada zuciyar su ta buga.
” Su ci gaba da yi, sai zuciyar su ta buga tukunna, Ni babu abinda ya dame daɗi kawai nake ji. Amma su c’su ci gaba da yi.
Wadannan sune kalaman da Emiefile yayi bayan ganawa da yayi da shugaba Buhari a fadar Aso Rock a Abuja kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta buga.
Sai dai kuma NAN ta ruwaito cewa akwai Emiefile ya garzaya fadar gwamnati ne domin ya shaida wa shugaban kasa cewa ya hakura da takarar shugaban kasa, zai ci gaba da zama a kujerar sa ta gwamnan Babban Bankin Najeriya.
Majiya ta sanar da NAN cewa Emiefile ya ysnke shawarar cigaba da zama a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, maimakon takarar shugaban kasa da tuni har wasu sun saya masa fom din takara ta naira miliyan 100.
Idan ba a manta ba kungiyoyin manoma sun hadu sun saya wa Emiefile fom ɗin takarar shugaban kasa a cikin makon jiya.
Sai dai kuma tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci duk wani jami’in gwamnati ko hadimin sa da ya fito takarar wata kujerar siyasa ya ajiye aiki wasu ke ganin sun yi gaggawar fitowa takarar.