Bayan wata kwaryakwaryar zama da aka yi tsakanin ƴan takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar APC da gwamnan jihar Nasir El-Rufai a gaban dan gwamnatin Kaduna, gwamnan ya zaɓi sanata Uba Sani ɗan takarar gwamnan sa a zabe mai zuwa.
Idan ba manta ba sanata Uba Sani da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar
Mohammed Sani Dattijo da Sanata Uba ne ke kan gaba wajen kamfen da neman goyon bayan gwamnan jihar don ɗayansu ya samu amincewar sa ya zama ma jam’iyyar ɗan takara.
A daren Laraba a wani taro da aka yi a tsakanin magoya bayan gwamna El-Rufai da sauran gaggan ƴan siyasan APC a jihar an kawo ƙarshen wannan batu.
Bayan El-Rufai ya zaɓi sanata Uba, ya kuma umarci Dattijo ya nemi takarar sanata wato kujerar da Uba Sani yake akai.
” Wannan shawara da gwamna kuma ubanmu duka ya yanke na amince da shi kuma muna fatan Allah ya sa shine mafi Alkhairi a garemu. Za mu cigaba da ga inda muka tsaya yanzu domin cigaban jam’iyyar mu ta APC.
” Na siya form din takarar gwamna amma kuma zan koma na siya ta neman Kujerar sanata. Fata na shine mu yi wa jama’a da jihar mu aiki tuƙuru domin cigaban mu, ƴan jihar mu da kasa baki ɗaya.
” Ina mai cigaba da miƙa godiya ta ga gwamna El-Rufai bisa daman da ya bani a tsawon aiki da nayi da shi tun daga farkon wannan gwamnati sannan kuma da jagoranci na gari da ya bamu ta hanyar koyarwa da dama wajen yin aiki a jihar Kaduna.
Sauran yan takarar da suka rage a jam’iyyar APC sun haɗa da Bashir Jamoh, Hinarabul Sani Sha’aban da sauransu. Idan ba su janye ba toh da su ne za a fafata a zaɓen fidda gwani wanda za a yi nan da kwanaki masu zuwa