Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya nada tsohon kakakin majalisar jihar Aminu Shagali mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa.
Wannan kujera ce Sanata Uba Sani ya rike kafin ya zama sanata a 2019.
Bayan haka gwamnan El-Rufai ya nada Hajiya Umma Ahmed, kantomar karamar hukumar Birnin Gwari Kwamishinan harkokin kananan hukumomin jihar.
Muyiwa Adekeye wanda shina ya sanar da wadannan nade-naden gwamnati a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce Umma za ta maye gurbin Dr. Shehu Muhammad, wanda ya ajiye aiki domin yin takarar kujerar siyasa.
Shi kuma Abdullahi Ibrahim wanda shine mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa zai canja Umma a Birnin Gwari.
Murtala Dabo kuma shine sabon mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tattalin arzikin jihar.
El-Rufai ya nada Dr Jibrin Alhaji babban sakataren hukumar majalisar dokokin jihar.