Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya shiga hannun hukumar EFCC bayan mamaye gidan da da jami’an tsaro suka yi tun karfe 11 na safe.
Jami’an tsaro sun zagaye gidan Sanata Okorocha dake ynguwar Maitama dake Abuja, sannan sun rika harba barkonon tsohuwa ga magoya bayan Okorocha a gidan sa a lokacin da suka kawo mamya gidan.
Sai dai kuma a lokacin da jami’an tsaro ke kokarin fito da Okorocha daga gidan sa ya tattauna da manema labarai in da ya ce” A na nema na ne ruwa ajallo domin a hana ni halartar zaman tantance ƴan takarar shugaban kasa da za ayi na jam’iyyar APC.
” Ba su so in halarci wannan zama. Shine ya sa suka aiko jami’an tsaro su zo su kama ni. Wannan shine kawai dalili amma babu wani abu bayan haka.
Sai dai kuma jami’an hukumar EFCC sun ƙaryata haka inda suka ce Okorocha ya tsallake belin kotu har sau biyu.
” Kotu ta yi zama domin sauraren karar da aka shigar akan sa amma a duk lokacin da aka bukaci ya bayyana a kotu sai ya ki zuwa. A karshe dai dole alkalin kotun ya ke ɗage zaman kotun.
” Da muka gaji da boye boyen da yake yi shine muka kama shi domin ya zo yayi mana bayani game da zargin wawushe biliyoyin kuɗaden talakawan jihar Imo da yai a lokacin ya na gwamna.
Discussion about this post