Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi, ya bayyana cewa duk da an yi wa tsohon Shugaban Riƙon EFCC, Ibrahim Magu ƙarin girma, idan kwamiti ya tabbatar da laifi a kan sa, sai an hukunta shi.
A cikin Yuli 2020 ne aka gurfanar da Magu gaban Kwamitin Ayo Salami, domin amsa zarge-zargen da Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi masa.
An kafa kwamitin bincike ƙarƙashin shugabancin tsohon Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, Ayo Salami, wadda tun bayan da ta kammala bincike ta miƙa rahoton ta ga Shugaba Muhammadu Buhari. Har yau shiru ka ke ji.
Bayan cire Magu, an maye gurbin sa da Abdulrasheed Bawa, wanda ya fito jiha ɗaya da ogan sa wanda ya shirya cire Magu, wato Ministan Shari’a Malami.
Bayan ƙarin girman da aka yi wa Magu kwanan nan, Dingyaɗi MInistan Harkokin ‘Yan Sanda ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa “har yanzu Hukumar ‘Yan Sanda ba ta ɗauki matakin hukunta Magu ba, kamar yadda kwamiti ya bayar da shawara. Amma ta ƙara masa girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, kafin ya kai ga yin ritaya.
“Wannan kuma batu ne Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ce ya kamata a ce ta duba lamarin ƙarin girman tuni, domin aikin ta ne.
“Ina da masaniya kuma cewa Hukumar PSC ɗin a ƙarƙashin Ofishin Shugaban Ƙasa ta ke.
“Abin da kawai Ni zan iya cewa, Magu dai ya riga ya yi ritaya. Wannan kuma batu ne da Hukumar PSC ce za ta iya yi maku wannan ƙarin bayani.
“Maganar rahoton kwamitin binciken Magu kuwa da ku ka tambaye ni, ban san matsayin gwamnati a kan sa ba. Amma dai ina jin ana duba yiwuwar ɗaukar hukuncin da ya dace.
“Kuma don ya yi ritaya ko an ƙara masa girma, ba ana nufin wai ba za a iya hukunta shi idan an same shi da laifi ba.”
Dingyaɗi ya ƙara da cewa nan da wata ɗaya ko biyu za a ƙara ɗaukar kuratan ‘yan sanda 10,000, domin ganin an ɗauki 40,000 ɗin da gwamnatin Buhari ta yi alƙawarin ɗauka aiki a zangon ta na biyu.