Dubun wani Kansila mai suna Abdulraman Adamu dake wakiltar Yankin Kibiya a karamar hukumar Soba ya faɗa hannun ƴan sanda bayan sun kamashi yana safarar bindiga AK 47 ga ƴan bindigan dake tabargaza a yankin Giwa.
Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana cewa jami’ai sun damke Adamu ne da dare wajen ƙarfe 8 na dare a bisa babur ɗauke da bindigar da harsasai zai a yankin karamar hukumar Giwa.
Bayan an tuhume sa sai aka gano zai kaiwa wasu ƴan bindiga ne da yake wa aiki a dajin.
Kwamishinan ƴan sandan Kaduna Yekini Ayoku ya ya ymarci jami’ai da du ci gaba da bincike har sai an gano gungun wasu mutanen da ke irin haka a jihar. Wato aiki da ƴan bindiga wajen gallaza wa mutane a zaba.
Yankin Giwa na daga cikin yankunan da hare-haren ƴan bindiga ya yi tsanani matuka a jihar Kaduna.
Discussion about this post