Bana a tarihin siyasar Jihar Jigawa babba jam’iyya kuma mai mulki ta bawa Jigawa Arewa maso Gabas wato yankin Hadejiawa takarar gwamna, Wanda a bisa tarihi babu wata jama’iyya wanda tayi hakan.
Kamar yadda na fada a baya, a cikin rubutu na MENENE ZUNUBIN BAHADEJE? A shekarun Jigawa babu wani daga yankin Hadejia da yayi gwamna a Jigawa, a misali Malam Sule Lamido a PDP yayi takarar gwamna sau biyu, yayi nasara, bayan ya sauka ya tsayar da Malam Aminu Ringim daga Arewacin Jigawa har sau biyu, amma a yau Jama’iyyar APC karkashin jagorancin Gov Abubakar Badaru ta bawa yankin Hadejia damar yin takarar gwamna a zabe mai zuwa, Malam Umar Namadi yayi nasarar cin zaben fidda gwani da gagarumar nasara, da dukkan alamu anzo lokacin da wannan yanki zaiyi gwamna a Jigawa.
Amma babbar jama’iyya mai adawa ta PDP a Jigawa a wannan karon ma ta maida takarar gwamna Jigawa ta tsakiya, wanda a sabon salo a wannan karon ma dan Baban jagorar ne Mustapha Sule Lamido zai gaje shi, duk da cewa dakarun sa na siyasa suna wannan yankin.
Duk da cewa bada takara ko yin takara ba shine yin gwamna ba. Amma tabbas alama ce da kuma tirba ta zama gwamna.
Adalci ne da kuma karfafa hadin kan mutanen Jigawa wajen sanyawa da bawa ko wane mutum da kowane yanki damar basu tasu gudunmawar wajen gina tasu jihar.
Tarihin Jihar Jigawa ya nuna irin gudunmawar da wannan yanki na Jigawa ta Gabas ta bada wajen ginawa da ci gaban Jigawa, kama ta samar kwararru a kowane fanni, gina tattalin arziki, noma da samar da masana’antu.
Wai Shin za a iya cewa a wannan karon za a iya cewa Badaru ya shafewa Hadejiawa hawayen su?
Discussion about this post