A ranar Alhamis ne dandazon kudan zuma suka kashe Ismail Hussaini dalibin makarantar firamaren Yanoko Nomadic dake karamar hukumar Tofa a jihar Kano.
Kawun mamacin Sanusi Dawakintofa ya sanar da wannan abin takaicin wa PREMIUM TIMES.
Dawakintofa ya ce mamacin ya ƙasa guduwa a lokacin da kudan zuma suka far masa saboda karayan da yake da ita a kafa a dalilin cutar sikila da yake fama da ita.
Dagacen Yanoko kuma Sarkin Fulanin kauyen Habibu Bello ya ce Hussaini ya rasu da rana bayan an yi gaggawar kai shi asibitin Tofa.
Gwamnatin jihar Kano ta bude makarantu 380 domin samar wa ‘ya’yan makiyaya Fulani da takalawa mazauna karkara ilimin boko.
Daga jihar Bauchi Kano ce jihar ta biyu fi yawan makarantun boko irin haka a Najeriya.
Discussion about this post