Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2023 a ƙarƙashin PDP, ya ragargaji gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce “maƙaryata da ‘yan-amshin-Shata ne kewaye da Buhari, shi ya sa bai samar da sauƙin da ya riƙa zuguguta cewa zai samar a Najeriya ba.”
Bala Mohammed ya bayyana haka ne a lokacin da ya dira Katsina wurin taron ganawa da wakilan zaɓen ‘yan takara, a ranar Lahadi.
Ya ce Buhari ya gaza matuƙa ta fannoni da dama, musamman wajen kasa samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya.
Ya ce a yanzu Najeriya a ruɗe ta ke, kuma a gigice al’ummar ƙasar su ke, saboda Buhari ba shi ma da kuzarin da zai iya tashi ya nuna shi shugaba ne mai iya yi, ko mai iya sawa a yi ko ya ce a bari, kuma a bari.
“Jihar Katsina na da tarihin samar da shugabanni nagari. Mun ga abin da marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua ya yi a zamanin sa. Amma shi Buhari bai kewaye kan sa mutanen da su ka cancanta ba, sai ya tattago gungun maƙaryata da ‘yan-amshin-Shata su ka kewaye shi.
“A kullum su na shirya masa ƙarairayi. Kuma kun san yadda soja ya ke. Bai san irin tuggu da kitimirmirar mutane ba, kuma bai san yadda gwamnati ke aiki ba. Bai san yadda ake tafiyar da gwamnati ba.
“Buhari ba ya shiga karkara cikin talakawa. Sai dai ya yi zaune a Fadar Shugaban Ƙasa, maƙaryata na kai masa ƙarairayi, shi kuma ya na yarda da duk abin da su sanar da shi.”
“Ƙasar nan sai ƙara ruɗewa ta ke yi, komai ya lalace, kai ka ce babu gwamnati kamar ana zaune kara-zube.
“Talauci da yunwa da ƙuncin rayuwa ya addabi jama’a. Matsalar tsaro sai ƙara lalacewa da taɓarɓarewa ta ke yi. Talakawan karkara ba su iya zuwa gonakin su, yara ƙanana na tsoron zuwa makaranta, mutane tafiye-tafiye na neman gagarar su.
“Nan a jihar Katsina ku ma ‘yan bindiga sun hana ku kwanciyar hankali, ku na jihar da Shugaban Ƙasa ya fito. Shin abin bai kasance maku tamkar wasan kwaikwayo ba? Abin kamar jami’an tsaro ba su san abin da su ke yi ba.” Inji Gwamna Bala.
Bala ya ce gaba-ɗayan shugabannin Arewa sun ji kunya, sun kasa ciyar da Arewa gaba, sun bar ta ciki matsaloli barkatai.
Discussion about this post