” Da ministoci sun san cewa Buhari zai yi masu irin wannan diran mikiya, da yawa daga cikin su da ba su yi gaggawar siyan fom ba. Duk sun ɗauka shike nan Buhari zai cigaba da aiki da sune har sai ya rage wata uku a yi zabe sai su ajiye aiki, amma Buhari yaya falle musu kafafu.
” Ko shi kansa ministan kwadago, Chris Ngige ba bu tabbacin cewa duk da ya janye takarar sa Buhari zai sake naɗashi minista.
” Ai kusan mako guda kenan Buhari ya hana su duka ministocin da suka sayi fom su gan shi. Sun nemi su yi masa yankan baya ne, su ci nasu su ci na wasu. Yaya za a yi haka kuwa. Buhari na sane kuma ya san takun su.
Waɗannan sune kalaman da wani babban makusanci Buhari a fadar shugaban kasa ya shaida wa PREMIUM TIMES ba tare da ya na din a bayyana sunan sa ba
Idan ba a manta ba ministan Shari’a, Abubakar Malami ya yi kokarin majalisa ta amince da wata sabuwar doka da ya kirkiro na a rika bari ministoci na cigaba da zama a kujerun su har sai an kusa kammala mulki zaɓe ya kusa.
Sai dai wannan kudiri ta sa ba ta tsallake majalisar dattawa ba. Tuni suka wancakalar da ita suka ce ya saba wa irin dokar da ya kamata ya shiga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Hakazalika, Malami ya saka cewa ya mika takardar yin murabus daga minista a shafinsa ta tiwita, amma kuma bayan ɗan wani lokaci ya goge.
Masu yin sharhi sun ce akwai yiwuwar Malami fa ya afka cikin ruɗani. Ya a son kujerar minista yana kuma son kujerar gwamna amma kuma bai shirya sauka daga kujerar ba yanzu haka.