Kwana ɗaya kafin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara Jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabas a ranar Alhamis, a wata ziyarar kwana biyu, ƙungiyar MASSOB ta ƙabilar Igbo gurguzu sun nemi a gaggauta sakin Nnamdi Kanu daga tsare shi da ake yi.
Daga nan kuma sun nemi lallai a bai wa ƙabilar Igbo damar yin shugabancin Najeriya a 2023.
MASSOB ta yi wannan kakkausan bayani ne a cikin wata sanarwa da shugaban ta Uchenna Madu ya sa wa hannu kuma ya fitar a ranar Laraba.
Kanu dai shi ne Shugaban IPOB da ke tsare ana ci gaba da shari’ar sa a Abuja, tun bayan da jami’an tsaron Najeriya su ka sungumo shi daga Kenya, cikin 2021.
Ana tuhumar sa da cin amanar ƙasa da kuma ta’addanci.
MASSOB da IPOB dai Ɗanjuma ne da Ɗanjummai. Dukkan su na hanƙoron neman kafa ƙasar Biafra, ta gurguzun zallan ƙabilar Igbo. Wato neman ɓallewa daga Najeriya, ta hanyar tashe-tashen hankula.
Yayin da Shugaban MOSSOB ya ce ba ya jayayya da ziyarar da Buhari zai kai a Ebonyi, amma ya ce sakin Nnamdi Kanu zai rage yawan tashe-tashen hankula da kashe-kashen da ake yi a yankin.
“Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwana biyu a Ebonyi, ina tabbatarwa da kuma tunatar da Shugaban Ƙasa cewa sakin Nnamdi Kanu ne kaɗai zai kawo sauƙin tashe-tashen hankula a Kudu maso Gabas.
“MASSOB na kuma tunatar da Shugaba Muhammadu Buhari cewa ci gaba da tsare Kanu a hannun DSS zai ƙara tunzirawa da ruruta wutar fitintinun kawai. Kuma zai kara munana tattalin arziki a yankin.”
Sannan kuma ya ce a bai wa ƙabilar Igbo damar zama Shugaban Ƙasa zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin a zaɓen 2023.
Buhari zai kai ziyara Ebonyi domin buɗe wasu ayyukan da Gwamnan Jihar ya yi.