Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa wanda zai mika wa mulki a 2023, mutum ne wanda ƴan Najeriya suka zaɓa.
Shugaba Buhari ya faɗi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Aso Rock bayan an sauka sallah Idi.
Ɗan jarida ya tambayi shugaba Buhari cewa ” Ƴan talarar shugaban kasa na ta zuwa wurinka neman yarda, kuma wasu sun ce kace muce su je su fito takara, wa za ka mika wa mulki a 2023?
Sai Buhari ya ce ” Duk wanda ƴan Najeriya suka zaɓa shine zan mika wa mulki.
Bayan haka kuma shugaba Buhari ya kara da yin tsokaci akan matakan da jami’an tsaron kasar nan suke ɗauka domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
” Duk manyan hafsoshin tsaron kasar nan da sufeto janar ɗin ƴan sanda na aiki tukuru domin ganin an kawo karshen matsalar ƴan ta’adda a kasar nan.
” Yanzu abinda muka saka a gaba shine muga yadda za akawo manoma tsaro domin damina ya tunkaro, a samu a koma gona.
A wannan shekara Shugaba Buhari ya garzawa tsohuwar filin Parade na Abuja domin yin sallar Idi.
Rabon da ayi sallah a wannan masallaci ya kai shekara uku tun ɓarkewar annobar Korona .
Bayan haka ƴan uwa da abokan arziki sun rika tururuwa zuwa fadar shugaban kasa domin gaisuwar sallah ga shugaba Buhari.