Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya maida wa Gwamnatin Tarayya zunzurutun kuɗaɗe har Naira miliyan 450, na watandar kuɗaɗen makaman da aka zargi Sambo Dasuƙi ya yi lokacin kamfen ɗin zaɓen 2015, domin PDP ta lashe zaɓen da ta sha kaye a lokacin.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da maida kuɗaɗen, waɗanda kuɗaɗen cinikin makamai ne waɗanda Sambo Dasuƙi ya yi watandar su a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Ayu wanda a yanzu shi ne Shugaban PDP na ƙasa baki ɗaya, ya fara mayar da rabin kuɗin cikin Oktoba, 2021, kamar yadda wannan jaridar ta tabbatar, kafin a zaɓe shi shugaban PDP. Kuma ya biya kuɗaɗen ne ta hanyar cek, wanda ya rubuta adadin kuɗaɗen da sunan Gwamnatin Tarayya.
Kwamitin Shugaban Ƙasa mai binciken bankaɗo kuɗaɗen makamai da aka yi wa ‘yan siyasa watandar su a lokacin gwamnatin Jonathan ya gano kuɗaɗen a hannun Ayu.
An dai zargi Sambo Dasuƙi ya yin watandar dala biliyan 2.1 na kuɗaɗen makamai da sunan kwangiloli na bogi domin a yi kamfen da kuɗaɗen lokacin zaɓen 2015, wanda Jonathan ya faɗi.
Majiya ta ce lokacin da Ayu ya riƙa ɓata lokacin biyan kuɗaɗen, kwamitin ya ƙwace wani danƙareren gidan da ya mallaka a Abuja. Amma an mayar masa da gidan bayan ya biya Naira miliyan 450 ɗin da aka yi masa watanda.
Wannan jarida ta nemi jin ta bakin Ayu a ranar Talata, amma bai amsa kiran da aka yi masa ba.
Discussion about this post