Daya daga cikin hakimai huɗu da mai martaba sarkin Zazzau ya dakatar daga hawan durbar Honarabul Suleiman Ibrahim Dabo Wakilin Birnin Zazzau, ya bayyana cewa akasi aka samu a lokacin da tawagar mahayansa suka zo wucewa gaban sarki a lokacin hawan sallah.
Da yake tartaunawa da PREMIUM TIMES, Dabo ya ce bashi ne da kansa yayi hawa ba bana wakilin sa ne yayi hawa kuma babu yan tauri a cikin tawagar.
” Ko da tawaga ta suka taso tun daga gida basu tare da ‘ƴan tauri, na saka a ɗauki bidiyon wannan hawa tun daga gida.
” Abinda ya auku shine a lokacin da tawaga ta suka iso kofa kafin su kai gaban sarki su wuce sai wasu ƴan tauri da bamu san su ba suka yi wuf suka shiga gaban tawagar suka rika wasa da wukake a gaban sarki. Amma ba mu ne muka yo gayyan su ba.
” Ni da kaina na ga sarki kuma na nuna wa masarauta bidiyon tawagata tun daga gida har zuwa inda ƴan taurin suka gwamutsu da tawaga ta.
Bayan haka Wakilin Birnin Zazzau, ya yi ƙarin haske akan dakatarwar da ake cewa an yi musu.
” Ba a dakatar da mu daga kujerun mu ba, an dakatar da mu ne daga hawa nan gaba har sai an kammala bincike da masarauta ke yi.
” A matsayina na ɗan majalisa na san muhimmancin kiyaye bin doka, saboda haka ba zan yi wani abu na karya doka ba.
Sauran hakiman da aka dakatar da su daga hawa sun haɗa da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris ɗan tsohon sarkin Zazzau marigayi Shehu Idris. Sai kuma Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo wand shine ɗan majalisan jiha dake wakiltar birnin Zariya da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.