Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi hannun riga da waɗanda suka siya masa fom ɗin takarar shugaban kasa yana mai cewa bai aike su ba.
” Jonathan bai aiki wani ya siya masa fom ɗin takarar shugaban kasa ba. Waɗanda suka yi karambanin yin haka ma basu kyauta ba kwatakwata ba.
Kakakin Jonathan, Eze, ya kara da cewa a cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata cewa Jonathan ya ce bai tsai da shawarar yin takara ba saboda haka bai aiki wani ya siya masa fom ba.
Ya kara da cewa yin haka da waɗannan kungiyar suka yi cin fuska ne ganin irin matsayin da ya rike a kasa ya cancanci ace an tuntube shi kafin a siya masa fom irin haka.
Idan ba a manta ba gamayyar kungiyoyi daga Arewacin Najeriya sun tara naira miliyan 100 sun siya wa Jonathan fom din takarar shugaban ƙasa ba tare da sanin sa ba.
Kungiyoyin sun bayyana dalilin yin haka cewa wai Jonathan shugaba ne nagari mai kishin kasa da ya cancanci ya dawo ya shugabanci Najeriya.
Sai dai kuma wasu lauyoyi a kasar nan sun nuna cewa doka ba ta ba Jonathan damar sake tsayawa takara a kasar nan.
Idan ba a manta ba shugaba Buhari na APC ya kada Jonathan a zaɓen 2015.
Discussion about this post