Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa al’ummar Jihar Katsina sun ga bala’in ‘yan bindiga, a cikin mummunan tashin hankalin da aka shiga matsananciyar wahala.
Masari ya ce bala’i ya yi tsananin da an fatattaki mutane daga yankunan su, har ta kai sama da Katsinawa 13,000 sun yi gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.
Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da ‘yan bindiga su ka hana zaman lafiya.
‘Yan bindiga sun kashe dubban mutane a Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja, Kebbi da Kaduna.
Sun kuma karɓi biliyoyin kuɗaɗen fansar waɗanda su ke yin garkuwa da su. Kuma sun kori dubban jama’a daga garuruwan su, sun kwashe masu dabbobi da kayan abinci, sun kuma hana su zuwa gona noma.
Wahala Ta Afka Wa Al’ummar Katsina:
Masari na magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda ya je a matsayin sa na ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC.
Fayemi ya je Katsina a ranar Lahadi, domin ganawa da wakilan zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa na jihar Katsina, domin ya nemi goyon bayan su.
Ya ce ‘yan Jihar Katsina, musamman waɗanda su ka yi iyaka ko maƙautaka da Dajin Rugu ne su ka fi ɗanɗana bala’in ‘yan bindiga.
“Mai Girma Gwamna, ka yi maganar yadda matsalar tsaro ta kassara jihar Katsina. To ina sanar da kai cewa farfaɗo da tattalin arziki a yankin da matsalar tsaro ta yi wa illa ya na da muhimmanci sosai. Wasu mutanen sun yi gudun hijira, wasu sun rasa komai sun danna cikin garuruwan da dangin su su ke su na zama da rayuwar takaici.”
“Kai ko a yanzu su ka koma yankunan su, to babu wani abin dogara domin su rayu da su ke da shi. Saboda an sace masu dabbobi.”
“A yanzu haka akwai ƙauyen da ake kira shimfiɗa a cikin Karamar Hukumar Jibiya. Bayan da ‘yan bindiga su ka kori mutanen garin. Sun banka wa garin wuta. Yanzu haka muna kashe naira miliyan 100 domin sake farfaɗo da garin shimfiɗa.” Inji Masari.
Discussion about this post