Duka da mutane na cigaba da yin jimamin kisan kiyashin da mahara suka t’yi a jihar Zamfara ranar Juma’a, ƴannbindigam sun sake afkawa kauyukan dake karkashin ƙaramar hukumar Maradun sun kashe mutune 7.
Maradun da Bakura kananan hukumomi ne dake da iyaka da juna.
‘Yan bindigan sun afka kauyukan Faru da Kauyen Minane ranar Asabar da rana tsaka.
Wani mazaunin karamar hukumar Jamilu Muhammad ya ce yana asibitin Maradun sai ya ga sojoji sun shigo da gawarwakin mutanen da ‘yan bindigan suka kashe.
“Mutanen mu dake Garin Minane sun ce maharan sun shigo da misalin karfe 2 na rana suna harbi ta ko ina.
” Dama kuma a baya idan maharan sun shigo su kan shiga gidajen mutane su saci dabbobi da kaya masu daraja amma wannan karon da suka shigo wuta kawai suka rika buɗe wa mutane.
“Maharan sun kashe mutum shida a Garin Minane mutum ɗaya a Faru.
“Akwai yiwuwar za a samu karuwa a yawan mutanen da aka kashe saboda har yanzu ba a ga wasu mutanen ba.
“An yi jana’izan mutanen da maharan suka kashe a Maradun saboda mutane na tsoran komawa kauyukan su.
Muhammad ya ce duk maza ne maharan suka kashe inda mutum hudu daga cikin su ‘yan bindigan sun kashe su a bayan kauyen Garin Minane yayin da suke hanyar dawowa daga gonna.