Hedikwatar Hukumar tsaron ƙasa DHQ ta bayyana cewa dakarun sojin Najeriya dake aiki a karkashin ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ‘yan bindiga 43, sun kama wasu mutum 20 sannan sun ceto mutum 63 da ‘yan bindigan suka yi garkuwa da su a Arewa maso Gabashin kasar nan a cikin makonni uku.
Darektan yada labarai na hukumar manjo-janar Bernard Onyeuko ya sanar da haka ranar Alhamis da yake bayani kan fafatawan da jami’an tsaro suka yi a kasar nan tun daga ranar 28 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu.
Onyeuko ya ce daga ranar 1 zuwa 14 ga Mayu Boko Haram 1,627 sun mika wuya ga jami’an tsaro.
Ya ce a cikinsu akwai maza 331, mata 441 da yara 855.
Onyeuko ya ce zuwa yanzu ‘yan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya.
Ya ce dakarun sun kashe Malam Shehu, Amir din Boko Haram tare da wasu mabiyan sa a Jaje, Mango Ali, Dissa, Balangaje.
Onyeuko ya ce sojojin sun kashe kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki da wasu mabiyansa a dajin Sambisa dake kauyen Yuwe a karamar hukumar Konduga.
Ya ce dakarun sun Kuma kama wani Modu Pantami shima da ke yi wa Boko Haram jigilar kayan abinci da sauransu.
“Dakarun sun kwato makamai da dama da suka hada da bindiga mai kiran ‘LMGS’ guda biyu, babban bindiga ƙirar AK-47 guda 21, bindiga kirar AK-56 guda 11, MG guda 22, harsasan bindiga masu girmar milimita 7.62 guda 419, bindiga kirar Turret guda daya, harsashin bindigar AK-47 guda 31, babura uku da Keke shida.
Sauran kayan da sojojin suka kama sun hada da injin ɗin ban ruwa daya,jigidan harsashi biyu da mota kiran Isuzu.
Onyeuko ya ce ‘Operation Whirl Stroke’ sun kashe ‘yan bindiga 13 a jihohin Benue da Taraba
Ya ce dakarun sun kwato harsasan bindiga 27, babur daya da wayoyin 8.
Discussion about this post