Idan ba a manta a cikin makonni biyu da suka wuce tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya ziyarci Kaduna domin ganawa da da gwamna da kuma wakilan jam’iyyar APC don neman kuri’un wakilan jam’iyyar.
A wajen wannan taro da ganawa da Tinubu yayi gwamna Nasir El-Rufa’i tare da wasu daga cikin jigajigan jam’iyyar sun har da wasu daga cikin wakilan jam’iyyar sun bayyana cewa Tinubu ne za du zaɓa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.
El-Rufai ya ce ” Tinubu namu kuma a kullum yana tare da mu. Saboda haka lokaci yayi da zamu saka masa da abinda yayi mana. Ina tabbatar masa cewa wakilan APCn Kaduna duk nashi ne.
Sai dai kuma gwamna El-Rufai da da wakilan Kaduna sun wancakalar da wancan alkawari a wajen taro irin haka da ɗaya daga cikin ƴan takarar ya kawo garin Kaduna.
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi Ɗan Amanar Daura, ya kawo irin wannan ziyara Kaduna domin neman goyon bayan gwamna El-Rufai da wakilan Kaduna su zaɓi Amaechi ɗan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar APC.
A jawabin da gwamna El-Rufa’i yayi, ya tabbatar wa Amaechi da goyon bayan sa da na duka wakilan APC daga Kaduna.
El-Rufai ya ce ” Mun yi wa wani alkawarin bashi kuri’un mu amma kuma mun canja shawara yanzu, Amaeci zamu yi kaf ɗin mu daga Kaduna. Mun fi ganin Amaechi ne zai kawo mana irin sauyin da muke so da kuma tsaro.
Hslascin da Amaechi yayi min da ba zan taɓa matawa ba
Gwamna El-Rufai ya kara da cewa gwamna Rotimi Amaechi yayi masa halascin da bazai taba mandatwa da shi ba.
” Akwai lokacin da jami’an tsaro SSS suka gayya ce ni ofishin su. Amaechi da ya ji haka ya garzayo hargida ya ɗauke ni a motarsa muka tafi can. Ya ce ba zai ofishin ba sai sun sake ni.
” Ina tabbatar muku da cewa a cikin motar sa ya zauna tsawon zaman da nayi a cikin ofishin SSS har sai da suka sake ni sannan muka tafi gida tare.
” Kai karshen magana ma ku sani shini duk duniya matata bata gwani irin Amaechi, saboda irin kulawa, ƙauna da kusantar da ke tsakani na da shi.
Bayan haka ne gwamna El-Rufai ya rangaɗana kuwaa, ya tambayi wakilai da jami’an gwamnati dake wajen waɗanda za su yi zaɓe cewa wa ye za su zaɓa tsakanin waɗannan ƴan takara da suka zo jihar, sai suka ce ,” Amaechi za su yi.
Mu a Kaduna Amaechi za mu – Zailani
Haka nan shima kakakin majalisar jihar Kaduna Yusuf Zailani, ya tabbatar wa Amaechi da sauran gungun tawagarsa cewa shi za su zaba a zaben shugaban ƙasa
” A jihar Kaduna fa mun gama koma, babu wanda zamu a zaɓen shugaban kasa idan ba Amaechi. Wannan shine shawarar da muka yanke muka haka za a ayi tafiyar, Amaechi kawai.
Sai dai kuma kamar yadda Tinubu ya zo jihar suka cika shi da romon baki suka ce sai shi, Amaechi ya zo yanzu, shima sun cika shi da romon baki sai shi sannan kuma har yanzu akwai sauran ƴan takara da ba su kawo irin wannan ziyara jihar ba ko yaya, oho!