Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi a Majalisar Tarayya, Abdulmumin Jibrin, ya fitar da sanarwar dalilan ficewar sa daga APC zuwa NNPP.
Jibrin, wanda na hannun daman ɗan takarar shugaban kasa ne, Bola Tinubu, ya ragargaji wani babba a ƙasar nan da ya ce shi ne dalilin ficewar sa, saboda ya na ƙoƙarin ganin ya kashe masa tasirin siyasa, tun lokacin dusashewar hasken ta bai yi ba.
Duk da Jibrin Kofa bai ambaci sunan babban da ya ke nufi ba, amma dai makusantan sa na cewa da Gwamna Ganduje na Kano ya ke.
Amma dai har yanzu PREMIUM TIMES ba ta kai ga tabbatar da hakan ba.
“Na Fice Daga APC Saboda Wani Babban Ɗan Gudubale Na Ƙoƙarin Kashe Hasken Siyasa Ta -Abdulmumin Jibrin:
“Tsawon shekaru 9 kenan ina sadaukar da dukiya ta da ilmi na da siyasa ta wajen ganin na taimaka wajen ciyar da APC a gaba.
“A matsayi na na Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, a cikin 2013, na yi kasadar jagorancin wakilan tarayya 60 daga PDP zuwa APC. Ni na samar da kuɗaɗen ɗaukar nauyin wurin da mu ka yi taron da haifar da gurguntawar da mu ka yi wa PDP mai mulki a lokacin.
“A lokacin na sha fama da ƙiyayya da barazana, bi-ta-da-ƙulli kala-kala daga gwamnatin PDP mai ci a wancan lokacin.
“A 2015 kuma na zama Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, an yi ƙulle-ƙullen da ya haifar da dakatar da ni a majalisa, tsawon shekaru biyu. A lokacin da na koma Majalisa, na samu shugabannin ta na faman rigima da gwamnati. A lokacin APC da gwamnati a lokacin.
“Ganin haka na tashi tsaye haiƙan mun kafa Ƙungiyar Kare Muradun Buhari a Majalisar Tarayya. A Majalisar Dattawa kuwa Sanata Abdullahi Adamu ne ya jagoranci wannan ƙungiya.”
Jibrin ya ce a lokacin da ya ci zaɓe a 2019, ya yi ƙoƙarin zama Kakakin Majalisar Tarayya, amma uwar jam’iyya ta taushi zuciyar sa, ta ce ya haƙura, za a yi karɓa-karɓa ne.
Ya ce haka ya haƙura, ya ci gaba da yi wa Kakakin Majalisar Tarayya na yanzu kamfen.
“Haka mu ka sadaukar da komai na mu ga jam’iyyar da ko na gode da Allah-sam-barka’ ba tayi mana ba, sai ma jefa mu a cikin kwandon shara da ta yi.”
Shugabancin Hukumar Gidaje Ta FHA Da Aka Ba Ni, Ba Wani Kayan Gabas Ba Ne -Abdulmumin Jibrin:
Jibrin ya ce kowa ya tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen 2019 na Majalisar Tarayya. Amma aka haɗa baki da wasu ƙusoshin jam’iyya aka yi masa yankan baya. A kotu kuma aka yi masa ‘shari’a-saɓanin-hankali.
“Bayan an ba ni shugabancin Hukumar Gidaje ta FHA, sai na gane ai hukumar ba wani kayan gabas ba ce, wurin cike ya yake da kitimirmira. Har ma gara majalisa da Hukumar FHA, muƙamin da dama na karɓa ne kawai don kishin ƙasa ta.”
Tsakani Na Da Ɗan Gudubalen Da Ke Neman Ganin Baya Na – Abdulmumin Jibrin:
Abu mafi firgitarwa da tayar da hankali da na fuskanta a cikin shekaru bakwai ɗin nan, shi ne yadda wani babban ɗan gudubale ke ta ƙoƙarin ya lalata ko ya tarwatsa duk wani wanda ya ke ganin wata barazana ce a wurin sa.
“Munin halayen wannan ɗan gubale ya kama da yadda Turawan Afrika ta Kudu su ka riƙan nuna wa baƙaƙen fatar ƙasar ƙiyayyar wariyar launin fata.
“A ƙarshe dai na zauna na yi karatun-ta-natsu, na ga har gara kawai na tashi na kare mutunci na daga bin wani ɗan gudubalen da a kullum shi so ya ke ya ga mabiyan sa na bauta masa. To ni ba zan zama bawa haka kawai don na yi wa wani biyayya ba. Ehe!”
Jibrin ya ci gaba da bayyana abin da ya kira tantagaryar rashin mutuncin da wannan babban ɗan gudubale ke gantsara masu a APC.
Ya ce kwanan nan sun yi doguwar magana ta waya, “har dai da na ga rashin mutuncin na sa ya kai ƙololuwa, na yi ta-maza na ce da shi, ‘yanzu kai a matsayin ka na uban mu a tafiyar siyasa, za ka yi farin ciki nan gaba idan ka ga mu na gantsara wa ‘ya’yan cikin ka irin rashin mutuncin da kai ka ke yi mana?”
Na Fice Daga APC, Na Ajiye Farantin Tallar Tinubu, Na Kama Kwankwaso:
Jibrin ya nuna matuƙar godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya ce zai riƙe shi a matsayin uba, har a bayan zaɓen 2023.
Sannan kuma ya yi sanarwar ficewa daga APC zuwa jam’iyyar NNPP, mai kayan marmari.
A ƙarshe ya ce ya ajiye tallar Bola Tinubu, tallar da ya ce ko da shi ko babu shi, Tinubu na da ‘yan talla masu yawan da ficewar Jibrin daga rukunin masu kamfen ɗin Tinubu ba zai rage kamfen ɗin da komai ba.
Discussion about this post