Shugaban jam’iyyar PDP Abdullahi Adamu ya sasanta tsohon gwamnan Zamfara, AbdulAziz Yari da gwamna mai ci Bello Matawalle.
A wata zama da aka yi eanar Litinin a Abuja Shugaban APC Adamu ya gana da dukkan su su biyu inda suka tattauna a tsakanin su sannan ya shiga tsakaninsu ya sasanta su.
Idan ba a manta ba a cikin watan Maris shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Zamfara ya sanar wa manema labarai cewa Yari da makarraban sa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Sai dai bayan haka sanata Kabiru Marafa ya sanar cewa an riga malam masallaci ne amma har yanzu basu koma PDP ba.